Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yi Sujjada Tare Da Fashewa Da Kuka A Wajen Daurin Aurensa

Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yi Sujjada Tare Da Fashewa Da Kuka A Wajen Daurin Aurensa

  • A wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an gano wani ango cikin taron jama'a a wajen daurin aurensa
  • Ana kammala daurin aure sai angon ya yi sujjadar godiya ga Allah sannan ya kuma fashe da kuka
  • Jama'a sun taya amaryar tasa murna domin sun ce wannan ya nuna yana matukar kaunarta

Ranar aure rana ce ta farin ciki ga ango da amarya domin ganin cewa mafarkinsu na son kasancewa tare ya zama gaskiya.

Kuma kowani bawa na da yadda yake nuna farin cikinsa, wani kan yi dariya idan wata ni’ima ta same shi yayin da wani kuma kan zubar da hawaye don nuna farin cikinsa.

Hakan ce ta kasance a bangaren wani ango da bidiyonsa ya yada a shafukan soshiyal midiya.

Ango na murna
Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yi Sujjada Tare Da Fashewa Da Kuka A Wajen Daurin Aurensa Hoto: beautifull_people_of_arewa
Asali: Instagram

A cikin wani bidiyo da shafin beautifull_people_of_arewa ya wallafa a Instagram, an gano angon yana sujjadar godiya ga Allah bayan an daura masa aure.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ana Tsaka Da Ruwan Sama, Tsoho Ya Rikewa Matarsa Lema Cike Da Kauna

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga nan kuma, sai matashin angon ya fashe da kuka inda abokansa da ke wajen suka garzaya inda yake tare da dago shi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Wannan abu da angon ya yi ya sa mutane tofa albakacin bakunansu inda wasu ke ganin lallai yana kaunar amaryar tasa, wasu kuma na ganin ya sha gwagwarmaya a yayin neman auren.

mooresoumaila ya yi martani:

"Allah ya kare su daga mugun ido Amen "

taskiiraa_ ya ce:

"Amaryarshi itace da godiya wannan ya nuna irin kaunarta da yakeyi"

kano_smart_house ya ce:

"Da kyar yasha wannan "

nanazaen_ ta rubuta:

"MashaAllah"

Ana Tsaka Da Ruwan Sama, Tsoho Ya Rikewa Matarsa Lema Cike Da Kauna, Bidiyon ya kayatar

A wani labari na daban, jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyana bidiyon wasu tsoffin ma’aurata biyu wanda ke nuna lallai sun sha soyayya a zamanin kuruciya.

Kara karanta wannan

Yadda Wata Amarya Da Kawayenta Suka Yi Shiga Ta Kamala, Bidiyon Ya Burge Mutane

A cikin bidiyon da shafin theotherelement ya wallafa a Instagram, an gano ma’auratan biyu wadanda suka tsufa tukuf-tukuf suna tafiya yayin da ake zuba ruwan sama.

An kuma gano mijin rike lema yana bin matar tasa cike da kulawa a kokarinsa na tabbatar da ganin cewa ruwan bai taba ta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel