Yan Bindiga Sun Kara Yin Awon Gaba da Mutane A Wani Babban Hanya A Najeriya

Yan Bindiga Sun Kara Yin Awon Gaba da Mutane A Wani Babban Hanya A Najeriya

  • Wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun tare babbar hanyar Enugu zuwa Port Harcourt inda suka yi garkuwa da dimbin fasinjoji
  • Yan Bindiga sun budewa motar sojojin da suka tunkare su wuta tare da raunata jami'an soji guda biyu
  • Mutane da dama sun samu raunuka daga harbin yan bindiga, yayin da masu motoci suka gudu suka bar ababen su

Jihar Enugu - An yi garkuwa da dimbin fasinjoji a ranar Asabar a lokacin da wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne, suka tare babbar hanyar Enugu zuwa Port Harcourt. Rahoton Premium Times

‘Yan bindigar wadanda adadinsu ya kai 30, an ce sun kai hari kan wasu motocin bas uku da ke kan hanyar tare da yin awon gaba da fasinjojin baki daya.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun budewa wata motar soji wuta tare da raunata sojoji biyu da suka yi yunkurin fafatawa da su, kafin daga bisani su tilasta wa dukkan mutanen da ke cikin motocin bas din uku cikin wani daji da ke kusa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da mazauna Abuja suka dage dole Buhari ya sauke ministansa da mai ba shi shawara

Abuja
Yan Bindiga Sun Kara Yin Awon Gaba da Mutane A Wani Babban Hanya A Najeriya FOTO Premium Times
Asali: UGC

Majiyoyi sun ce lamarin ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ce matafiyar da suka ga 'yan bindigar sunyi tunanin jami'an 'yan sanda ne da kafa shingen binciken motoci a hanya.

Wasu daga cikin matafiyan da suka fito daga cikin motocinsu domin sanin musabbabin tsaikon da aka yi a kan hanyar, sai ‘yan bindigar suka bude wuta kan motar sojojin, kamar yadda wani shugaban matasan unguwar ya bayyana.

Ya ce wasu mutane sun samu raunuka daga harbin yan bindiga, yayin da wasu suka gudu suka bar motocinsu.

Kwamishinan yada labarai na jihar Abia, Chikamnayo Eze, ya tabbatar da faruwar harin.

Kakakin ‘yan sandan jihar Abia, Geoffery Ogbonna, bai amsa kiran da aka yi masa ba da kuma sakon tes da aka yi masa na neman karin bayani.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun shiga wata jihar Arewa, sun hallaka 'yan kasuwa, sun sace matafiya 14

Amurka Ta Kashe Ayman al-Zawahiri, Mutum na Biyu ga Osama Bin Laden

A wani labari kuma, Shugaba Joe Biden, a jawabin da yayi wa manema labarai a yammacin jiya, ya ce umarnin kai hari da ya ba jiragen yakin Amurka a birnin Kabul na Kasar Afganistan yayi sanadiyar kashe al-Zawahiri.

Al-Zawahiri ya kasance jagora na farko ga tsohon shugaban Al-Qaeda, Osama bin Laden, wanda sojojin Amurka suka kashe a lokacin da yake buya a Pakistan a shekarar 2011.

Asali: Legit.ng

Online view pixel