An Kori Dan Sandan Da Aka Nadi Bidiyonsa Yana 'Halasta' Wa Kansa Karbar Cin Hanci

An Kori Dan Sandan Da Aka Nadi Bidiyonsa Yana 'Halasta' Wa Kansa Karbar Cin Hanci

  • Rundunar yan sandan Najeriya ta kori jami'inta Richard Gele wanda aka nadi bidiyonsa yana cewa baya kunyar karbar cin hanci kuma baya karbar kadan
  • An tube wa, Richard Gele, mai muƙamin sufeta kayan dan sandansa aka kuma sallame shi daga aikin nan take bayan kwamitin ladabtarwa ta same shi da laifi
  • Sufeta Janar na yan sanda, Alkali Baba, ya gargadi jami'an rundunar su guji aikata duk wani abu da ya saba wa dokar aiki su zama jarumai kuma masu nuna kwarewa wurin aiki

Rundunar yan sandan Najeriya ta kori Richard Gele, Sufetan dan sanda da aka kama a bidiyo yana 'halasta' kwatar kudi daga hannun mutane a ranar 25 ga watan Yuli, rahoton jaridar Leadership.

Dan sanda da aka kora.
An Kori Dan Sandan Da Aka Nadi Bidiyonsa Yana 'Halasta' Wa Kansa Karbar Cin Hanci. Hoto: @leadershipNGA.
Asali: Facebook

Sufetan, mai lamba AP/No. 188547, kafin korarsa, yana aiki ne da Mobile Police Mobile Force 77 Squadron, Okene Jihar Kogi, kuma aka kai shi aiki hanyar Itobe - Anyigba don tabbatar da tsaron lafiyar matafiya a lokacin da abin ya faru.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kashe Kwamandan Jami'an Tsaro A Jihar Arewa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dan sandan da aka kora, ɗan asalin jihar Benue ne kuma ya shiga aikin dan sandan ne a shekarar 2000.

An kore shi ne bayan kwamitin ladabtarwa na rundunar ta same shi da laifin bisa tuhumar da aka masa a karkashin dokar aikin dan sanda.

Sanarwar da CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ta ce;

"Daga yau shi ba jami'in rundunar yan sandan Najeriya bane. An tube masa kaya an kuma mika shi hannun kwamishinan yan sandan jihar Kogi, don daukan sauran matakai."

Sufeta Janar na yan sandan Najeriya, Alkali Baba, ya gargadi jami'ai su guji yin kwace, rashin ɗa'a, karbar cin hanci da sauran abubuwan da ba su dace ba yana mai cewa ba zai lamunci hakan ba.

IGP din ya bukaci su da su rika nuna halin jarumta da kwarewa wurin gudanar da ayyukan su.

Kara karanta wannan

Kano: Hotunan ragargazajjen asibiti inda mata ne tafiyar 3Km don zuwa haihuwa, ya tada hankalin jama'a

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel