Rundunar sojin Najeriya ta Sauya Fasalin Manyan Hafsoshinta

Rundunar sojin Najeriya ta Sauya Fasalin Manyan Hafsoshinta

  • Tabarbarewar tsaro yasa ta sauya wa wasu manyan Dakarun ta da hafososhi da kwamandoji wureren aikin su
  • Manyan sojojin Najeriya sun sheda wa Buhari cewa sun bullo da sabbin dabaru da zai tunkari matsalar tsaro da kasar ke fuskanta
  • A jiya Alhamis da daddare wasu 'yan bindiga sun kai hari shingen bincike na sojoji da ke kusa da dutsen Zuma

Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta sauya wa wasu manyan Dakarun ta wanda suka hada da Hafososhi da Kwamandoji wuraren aikin su. Rahoton BBC

Rundunar ta ce, tayi sauye-sauyen ne dan kokarin inganta ayyukan su yayin da matsalar tsaro ta ci gaba da tabarbarewa a Najeriya.

Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, Darektan hulda da jama'a na sojojin Najeriya ya ce babban hafsan sojin Najeriyar Laftana Janar Faruk Yahaya ne ya ba da umarnin sauye-sauyen.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro ta Ta’azzara, Shugaban Sojoji ya girgiza gidan Soja, an Taba Janarori

Ko a jiya Alhamis da daddare wasu 'yan bindiga sun kai hari shingen bincike na sojoji da ke kusa da dutsen Zuma, a Madalla ta jihar Naija dab da iyaka da babban birnin tarayya Abuja.

Miitary
Rundunar sojin Najeriya ta Sauya Fasalin Manyan Hafsoshinta Legit.NG

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan shugabannin tsaron Najeriya sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis akan tabarbarewar tsaro a Najeriyar.

Manyan sojojin Najeriya sun sheda wa Shugaban kasa cewa sun bullo da sabbin dabaru da zai tunkari matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

Ko a jiya Alhamis 'yan bindiga sun kai hari shingen bincike na sojoji da ke kusa da dutsen Zuma, a Madalla ta jihar Naija dab da iyaka da babban birnin tarayya Abuja.

Manyan hafsoshin Soji da aka yi wa garambawul sun hada da

Manjo Janar UT Musa daga hedikwatar sojoji ta runduna ta 81 zuwa hedikwata ta runduna ta 82 inda aka nada shi a matsayin babban kwamanda (GOC).

Kara karanta wannan

Martanin gaggawa: Sojoji sun sheke tsageru 30 da suka kai kan jami'an fadar Buhari

Manjo Janar TA Lagbaja daga hedikwatar runduna ta 82 zuwa hedikwatar runduna ta 1, inda yanzu ya zama babban kwamandanta.

Manjo Janar AS Chinade daga depo ta rundunar soji zuwa hedikwatar sojojin ta runduna ta 2, inda aka nada shi babban kwamanda.

Wadannan sune Manyan hafsoshin sojojin kasar da aka yiwa garanbawul

Karin Naira Biliyan 900 Domin Dakile Matsalar Tsaro Yayi Kadan – Lawan

A wani labari kuma, Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmad Lawan ya ce Naira biliyan 900 da aka ware don yaki da rashin tsaro a kasar yayi kadan.

Rahoton Daily Trust Lawan, ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga ‘yan majalisa gabanin dage zaman majalisar dattijai domin hutun shekara, inda ya koka kan yadda ‘yan ta’adda ke kashe-kashe da nakasa ‘yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel