Karin Naira Biliyan 900 Domin Dakile Matsalar Tsaro Yayi Kadan – Lawan

Karin Naira Biliyan 900 Domin Dakile Matsalar Tsaro Yayi Kadan – Lawan

  • Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmad Lawan ya ce Naira biliyan N900 da aka kara don yaki da rashin tsaro a kasar yayi kadan.
  • Ahmed Lawan ya ce ya zama dole suyi takatsasan wajen sauke hakkin alummar kasar da ya rataya a wuyansu musamman fanin tsaro
  • Senata Ahmed Lawan ya ce za su ba wa Sojoji da sauran jami'an tsaron kasar duk wani agaji da suke bukata

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmad Lawan ya ce Naira biliyan 900 da aka ware don yaki da rashin tsaro a kasar yayi kadan. Rahoton Daily Trust

Lawan, ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga ‘yan majalisa gabanin dage zaman majalisar dattijai domin hutun shekara, inda ya koka kan yadda ‘yan ta’adda ke kashe-kashe da nakasa ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Ku kiyayi Abuja, akwai matukar hatsari a cikinta: 'Dan majalisa ya gargadi abokan aikinsa

Ahmed Lawan ya ce matsalar tsaro yana damun sa sosai, korafin kuwa a duk tarukan da suke gudanarwa shine matsalar tsaro.

Ahmed
Karin Naira Biliyan 900 Domin Dakile Matsalar Tsaro Yayi Kadan – Lawan FOTO PUNCH
Asali: UGC

Senatan yace dole a matsayin su na Gwamnatin Tarayya su yi takatsantsan dan sauke hakkin da ya rataya a wuyan su, musamman kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Matsalar tsaro abu ne mai matukar wahala da kalubale, musamman cikin kwanakin nan da hare-hare da kashe-kashen mutanen kasar ya karu.
“A matsayin mu na wannan gwamnati, za mu ba duk wani gudunmawa da sojojin da sauran hukumomin jami'an tsaro ke bukata.
“A karin kasafin kudin shekarar 2022, mun karawa hukumomin tsaro Naira biliyan 900 .
"Mun san cewa ba zai ishe su ba, amma kudin zai yi matukar tasiri a gare su, muna sa ran hukumomin tsaron mu za su yi aiki fiye da yadda suke yi a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wasu 'yan majalisu sun shiga ganawar sirri don tattauna batun tsige Buhari

Ahmed Lawan ya kuma sanar da ‘yan majalisar cewa za a iya kiransu aiki lokacin hutu idan bukatar hakan ta taso.

Sanatocin Jam'iyyun Hamayya Sun Fice Daga Majalisa Bayan Kira a Tsige Buhari

A wan labari kuma, Sanatocin jam'iyyun hamayya sun fice daga zauren majalisar Dattawa biyo bayan kira a tsige shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari daga kujerarsa.

Channels TV ta ruwaito cewa hakan ya biyo bayan wata Dirama da ta auku a zaman mambobin majalisar Dattaawa ta ƙasa yau Laraba a Abuja, babban birnin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel