Yan Najeriya Sun Gaji Da Barazanar Tsaro, Sun Fara Tunanin Kare Kansu, NSA

Yan Najeriya Sun Gaji Da Barazanar Tsaro, Sun Fara Tunanin Kare Kansu, NSA

  • Gwamnatin tarayya ta amince talakawan kasa sun kai maƙura game da barazanar tsaro har sun fara neman ɗaukin kare kai
  • Mai bada shawara kan tsaro na ƙasa, NSA Babagana Monguno, ya ce gwamnati ta fara aiki kan sabbin dabarun kawo karshen matsalar
  • Shugaba Buhari ya kira taron gaggawa kan tsaro ne yau a fadarsa dake birnin tarayya Abuja

Abuja - Gwamnatin tarayyan Najeriya, a ranar Alhamis, ta amince cewa matsalar tsaron da ake fama da ita sassan ƙasar nan ta kai yan Najeriya bango, sun gaji da ita.

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) shi ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai bayan taron majalisar tsaro a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Bariki ba riba: Bayan shekaru 6 da barin gida, budurwa ta koma da cutukan kanjamau da TB

NSA Babagana Monguno.
Yan Najeriya Sun Gaji Da Barazanar Tsaro, Sun Fara Tunanin Kare Kansu, NSA Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

NSA ya bayyana cewa taɓarɓarewar tsaro ka iya jawo mazauna ƙasar su fara fafutukar neman kare kan su, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Haka zalika ya sanar da cewa yanzu haka gwamnatin ta duƙufa aiki da dare ba rana kan sabbin dabarun da zasu kawo ƙarshen matsalar tsaro baki ɗaya a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, majalisar koli ta tsaro ta amince da wasu sabbin dabaru domin ganin bayan matsalar, ya tabbatar da cewa za'a ƙara matsa kaimi kan ayyukan ta'addanci.

Monguno ya ce Najeriya ta tsinci kanta cikin wani yanayi mai muni, inda ya ƙara da cewa shugaban ƙasa na sane da damuwar talakawa game da yaɗuwar ƙalubalen tsaro.

Babagana Monguno ya ce:

"Mambobin hukumomin tsaro sun bayyana cewa a makonni masu zuwa, sun fara aiki kan sabbin dabaru da zasu kawo ƙarshen waɗan nan rikice-rikicen."

Kara karanta wannan

'Dan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Bayyana Buhari A Matsayin Mataimakinsa A 2023

"Sun yi wa shugaban ƙasa alƙawarin cewa za'a samu canji a yanayin fuskantar lamarin, duk da suna fuskantar iyakar da aka ƙayyade musu. Sun fahimci nauyin da ke kan su."

Matakin da zamu ɗauka kan harin Kuje - NSA

A cewarsa, nan ba da jimawa ba majalisar zata kammala bincike na musamman kan harin da yan ta'adda suka kai gidan Yarin Kuje ranar 5 ga watan Yuli, wanda ya yi sanadin tserewar mambobin Boko Haram da ke tsare.

Ya tabbatar da cewa za'a hukunta duk wanda aka gano, saboda wasa da aiki, har ya yi sakaci yan ta'addan suka tsere, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

"Muna cikin yanayi mai wahala, majalisar ta gano shugaban ƙasa ya fahimci damuwar mutane game da ƙaruwar matsalar tsaro. Na san mutane sun gaji, sun fara kokarin neman taimakon kare kai."

A wani labarin kuma Sanatoci na barazanar tsige shi, Shugaba Buhari ya naɗa suruƙinsa da wasu mutum biyu a manyan muƙamai

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Buhari ya yi martani kan barazanar tsige shi da sanatocin PDP suka yi

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin wasu mutum uku a matsayin shugabannin wasu hukumomin tarayya.

Mutanen da shugaban ya naɗa sun haɗa da Tijjani Ƙaura, Mista Augustine Umahi da kuma Kaftin Junaid Abdullahi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel