Karuwa Ta Sharbe Farjin Takwararta Da Reza Bayan Fada Ya Kaure Tsakaninsu Kan Kwastoma, Ta Shiga Hannu

Karuwa Ta Sharbe Farjin Takwararta Da Reza Bayan Fada Ya Kaure Tsakaninsu Kan Kwastoma, Ta Shiga Hannu

  • Wata karuwa yar Najeriya ta shiga hannun yan sandan Ghana bayan fada da ya shiga tsakaninta da takwararta kan kwastoma
  • Bellas ta yi amfani da reza wajen sharbe gaban abokiyar sana'arta saboda ta kwace mata daduronta wanda ya fi kowa biya mai kyau
  • Tun farko ta gargadi wacce abun ya ritsa da ita kan ta rabu da saurayin nata ko kuma ta dauki mummunan mataki a kanta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rundunar yan sandan kasar Ghana sun kama wata ‘yar Najeriya da ke karuwanci a yankin Ashanti kan zargin amfani da reza wajen yanke farjin abokiyar sana’arta.

Mai laifin wacce aka bayyana a matsayin magajiya uwar dukkan karuwai a Dichemso Plaza ta kuma yi amfani da rezan wajen yayyaga fuska da cinyoyin matar kan zargin ta kwace mata daduronta, shafin LIB ya rahoto.

Kara karanta wannan

Mahaifiya ta Umarci Danta Ya Rabu da Amarya Sa Tsaka Da Daurin Aure Saboda Tayi Mata Muni

An tattaro cewa wacce ake zargin mai suna Bella, ta gargadi takwarar tata mai suna Ruth da ta rabu da wannan mutumin saboda shine babban kwastomanta.

Yan sanda
Karuwa Ta Sharbe Farjin Takwararta Da Reza Bayan Fada Ya Kaure Tsakaninsu Kan Kwastoma, Ta Shiga Hannu Hoto: BBC.com
Asali: UGC

Hakazalika an ce ta yi barazanar sauyawa Ruth kamanni idan har ta ki jin gargadinta na rabuwa da daduron nata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kuma, ita wanda abun ya ritsa da ita ta ki jin gargadin, hakan yasa Bella da wasu mutum hudu suka tare ta a hanya sannan suka tikata da kasa.

Daga bisani sai suka rirrike hannaye da kafafunta inda suka ba Bella damar yayyaga mata fuska da farjinta.

Har yanzu ba a kama sauran mutum hudu da suka aiwatar da muguntar tare ba domin sun tsere bayan da suka samu labarin kamun Bella.

Bidiyon yadda karuwa ta dira daga bene mai hawa 5 bayan budurwar matashi ta bayyana a otal

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda karuwa ta dira daga bene mai hawa 5 bayan budurwar matashi ta bayyana a otal

A wani labarin, wani bidiyo da ke tashe a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ya bai wa jama'a da dama mamaki.

A bidiyon, an ga yadda karuwa ta diro daga bene dogo mai hawa biyar ba tare da ta ji ciwo ba sakamakon kokarin da take na rufawa kanta asiri.

A bidiyon da ya yadu, karuwar ta sauka ta bayan bene mai hawa biyar daga dakin otal da matashi ya kama mata suka kammala abinda zasu yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel