Tsaka da daurin Aure, Ango ya rabu da Amaryar Sa saboda Uwar sa ta ce ta yi muni

Tsaka da daurin Aure, Ango ya rabu da Amaryar Sa saboda Uwar sa ta ce ta yi muni

  • Wani ango a kasar Tunisiya yabi umarnin Mahaifiyar sa ya rabu da amaryar sa ana tsakiyar bikin daurin aurensu saboda ta yi mata muni
  • Hotuna Sun nuna Amarya tana murmushi sanye da rigar aurenta a lokacin da ta tsaya kusa da angonta wanda ke goge mata gyale da kyalle
  • Mahaifiyar Angon da Ta Umarci Danta Ya Rabu da amarya sa lokacin bikin daurin auren su ta ce bata taba ganin amaryar a fili ba sai dai a hoto

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani ango ya rabu da amaryar sa ana tsakiyar bikin dauren aurensu bayan mahaifiyarsa ta dakatar da sha’anin saboda surukarta ba ta da kyan gani. Rahoton THE NATION

Angon wanda ba a bayyana sunansa ba a kafafen yada labarai ya rabu da amaryar sa 'yar kasar Tunusiya bayan mahaifiyarsa ta umarce shi ya rabu da ita saboda bata da kyawun gani.

Kara karanta wannan

Bidiyon Rahama Sadau Tana Zuba Yaren Indiyanci, Za Ta Fito A Shirin Bollywood

An fahimci cewa har zuwa ranar bikin, mahaifiyar angon bata taba ganin amarya dan ta a fili ba sai dai a hoto kawai.

Amaraya
Tsaka da daurin Aure, Ango ya rabu da Amaryar Sa saboda Uwar sa ta ce ta yi muni FOTO THE NATION
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bride
Tsaka da daurin Aure, Ango ya rabu da Amaryar Sa saboda Uwar sa ta ce ta yi muni FOTO THE NATION
Asali: UGC

Amma da ta ga fuskarta da jiki, sai aka ce ta umurci danta da ya dakatar da hidimar saboda amaryar tasa ta yi "gajarta" kuma "mummuna ce".

Hotunan da aka fara hidimar sun nuna Amarya Lamia Al-Labawi tana murmushi sanye da rigar aurenta a lokacin da ta tsaya kusa da angonta wanda ke goge mata gyale da kyalle.

Amaryar ta ce ta kadu da kin amincewa da aka yi mata, kuma yana da wuya ta iya haduwa da mutane da kuma jin rade-radin su.

Yadda Cutar Kansa Ta Sauya Wani Matashi Mai Jini A Jika, Hotunansa Za Su Tsuma Zuciyar Kowaye

A wani labari kuma, Wani matashi mai suna Hashim Raza ya hadu da ibtila’i na rashin lafiya wanda ya kai har halittan jikinsa sun sauya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja Za Ta Haramta Karuwanci, Wasu Mata Da Ke Harkar Sun Magantu

Likitoci dai sun gano cewa Raza na dauke da cutar kansar ciki da na kayan ciki wanda har sun kai mataki na '4', shafin Convert to Islam ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel