Bidiyon yadda karuwa ta dira daga bene mai hawa 5 bayan budurwar matashi ta bayyana a otal

Bidiyon yadda karuwa ta dira daga bene mai hawa 5 bayan budurwar matashi ta bayyana a otal

  • Bidiyon karuwa tana dira daga bene mai hawa biyar a gigice domin tserewa budurwar matashin da ya dauketa haya ya bayyana
  • A bidiyon da tuni ya yadu, an ga karuwar da babu wasu kaya a jikinta tana direwa ta baya, sakamakon zuwan ba-zata da budurwar wanda ya dauketa tayi
  • Sai dai a wani mataki, an kusa samun rashin sa'a tunda ta kusa subucewa ta fado kasa inda aka ji ta tana ihun wayyo Allah

Wani bidiyo da ke tashe a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ya bai wa jama'a da dama mamaki.

A bidiyon, an ga yadda karuwa ta diro daga bene dogo mai hawa biyar ba tare da ta ji ciwo ba sakamakon kokarin da take na rufawa kanta asiri.

Kara karanta wannan

Bidiyon mace mai nishadantarwa sanye da hijabi a wani chasu ya janyo maganganu

Side Chick
Bidiyon yadda karuwa ta dira daga bene mai hawa 5 bayan budurwar matashi ta bayyana a otal. Hoto daga @DailyLoud
Asali: Twitter

A bidiyon da ya yadu, karuwar ta sauka ta bayan bene mai hawa biyar daga dakin otal da matashi ya kama mata suka kammala abinda zasu yi.

Karuwar da rabin jikinta tsirara ne a bidiyon, ta yi wannan dirar ba-zatan ne bayan asalin budurwar matashin ta bayyana babu zato balle tsammani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bidiyon ya nadi lokacin da karuwar ta kusa faduwa yayin da take taka-tsan-tsan wurin sauka daga benen a hawa na karshe.

Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani mai suna @DailyLoud ne ya fitar da bidiyon a ranar 25 ga watan Yuli wurin karfe 5 na yammaci.

Kalla bidiyon a kasa:

A daidai lokacin da ta kawo hawa na daya, an ji ta kurma ihun "wayyo Allah" sakamakon kusa subucewar da tayi ta fado kasa.

Wani mutum ya nadi bidiyon matar makwabcinsa da ta kai kwarto daki, tana kokarin fitar dashi

Kara karanta wannan

Jarumar Mata: Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

A wani labari na daban, wani mutum ya nadi bidiyon matar makwabcinsa yayin da ta gama shagalinta da kwartonta kuma tana son fitar da shi daga gidan.

Makwabcin wanda ya ga abinda ya faru kuma ya yanke hukuncin nadar lamarin a wayarsa daga dakinsa, ya bayyana irin cin amanar da matar tayi wa mijin ta.

Ma'auratan suna zama ne a rukunin gidaje wanda ke dauke da dakunan mutane da yawa, hakan ne yasa fitar kwarton matar ya nemi ya basu wuya.

Idan yace zai diro shine kawai hanyar da zai fita cikin sauki, amma kuma kwarton ya bayyana a rude kuma tsoro ya bayyana a fuskarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel