Gwamna Zulum Ya Yiwa Almajirin Borno da Ya Kirkiri Taraktan Hannu kyautar N5m

Gwamna Zulum Ya Yiwa Almajirin Borno da Ya Kirkiri Taraktan Hannu kyautar N5m

  • Gwamnan Jihar Borno ya yiwa wani matashi almajiri da ya kirkiri Tractan Hannu kyautar miiyan biyar N5m
  • Zulum ya bayyana farin ciki da ya hadu da Injiniyan da bai taba zuwa makarantar boko ba sai dai na Tsangaya ya kirkiri Tractan hannu
  • Laminu ya yi amfani da abubuwan da ke cikin injin din lister wanda asalinsa an yi shi ne don famfo ruwa wajen kera garma mai aiki kamar tarakta wanda ake turawa da hannu

Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum a jiya, Laraba, ya bayar da kyautar Naira miliyan biyar (N5m) don tallafawa fasahar wani almajiri mai hazaka a jihar Borno, wanda ya kera injin din garma. Rahoton Facebook The Govrnor Of Borno

Galibi ana haɗa garma da tarakta ne, da wasu na’urorin sufuri, ko kuma a ja su da hannu a gonaki.

Kara karanta wannan

An kai wa 'Dan Majalisar Daura, 'Danuwan Shugaba Buhari Hari Har Gida a Katsina

Zulum, wanda farfesa ne a fannin noman ban ruwa, ya ji dadin yadda Laminu Mohammed, dan shekara 25 daga karamar hukumar Gubio da ke arewacin jihar Borno, da bai taba zuwa wata makarantar boko ba sai ilmin addinin Musulunci na gargajiya da ake kira Tsangaya a Borno ya kirkiri Tractan hannu.

Zulum
Gwamna Zulum ya yiwa almajirin Borno da ya kirkiri tarakta hannu kyautar N5m
Asali: Facebook

Laminu ya yi amfani da abubuwan da ke cikin injin din lister wanda asalinsa an yi shi ne don famfo ruwa, wajen kera garma mai aiki kamar tarakta wanda ake turawa da hannu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani jami’in gwamnati ne ya sanar da Zulum basirar Laminu.

Zulum wanda injiniya ne, ya gayyato Laminu, suka tattaunawa game da fasahar, inda almajirin ya nuna kwarewarsa a kan kirkirar da yayi, daganan aka ba shi kyautar N5m.

Gwamnan ya ce kudaden na da nufin zaburar da ‘injiniyan da bai je makarantar boko ba da samar da karin garma da kirkiran wasu injunan noma wanda manoman jihar Borno zasu amfana da shi.

Kara karanta wannan

Gwamnan arewa ya raba tsabar kuɗi miliyan N172m da abinci ga talakawa 30,436 a karamar hukuma ɗaya

Tallafin Zulum ga Laminu ya zo ne makonni biyu bayan Gwamnan ya amince da sama da N5m ga wani matashi dan shekara 13 da ya yi amfani da laka wajen zana gadar sama ta farko a Borno da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Gamboru Ngala.

A wani labarin kuma, Zulum ya bayar da kyautar kananan motocin bas guda biyar da tsabar kudi N20m ga wani matashi dan jihar Borno da ya kware wajen mayar da motocin bas da injinan mai zuwa motocin lantarki masu amfani da hasken rana.

An ba da tallafin ga Kamfanin Phoenix ne mallakar mai cin gajiyar.

Najeriya tana da Shugaba Rago Wanda Bashi Da Kulawa - Odinkalu

A wani labari kuma, Tsohon Shugaban Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Najeriya, Farfesa Chidi Odinkalu, ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin "Shugaba Rago kuma Mai Halin Ko'inkula ".

Rahoton Daily Trust Lauyan kare hakkin dan Adam ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan halin rashin tsaro a Najeriya a cikin shirin Sunrise Daily na Channels Television a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel