An kai wa 'Dan Majalisar Daura, 'Danuwan Shugaba Buhari Hari Har Gida a Katsina

An kai wa 'Dan Majalisar Daura, 'Danuwan Shugaba Buhari Hari Har Gida a Katsina

  • A makon da ya gabata ake zargin wasu ‘yan iskan gari sun kai wa Hon. Fatuhu Mohammed hari
  • Mai taimakawa Honarabul Fatuhu Mohammed a kan harkokin Majalisa, ya tabbatar da lamarin
  • Ahmad Ganga yace da yamma wasu suka dura gidan ‘Dan majalisar da nufin za su ga bayan shi

Katsina - Mun samu labari cewa wasu miyagu sun kai wa Hon. Fatuhu Mohammed hari, yanzu haka ‘dan majalisar wakilan tarayya ne mai-ci.

Ahmad Ganga, wanda Hadimin ‘dan majalisar ne, ya bayyana wannan a shafinsa na Facebook tun a ranar Asabar da ta wuce, 23 ga watan Yuli 2022.

Kamar yadda Ganga ya bayyana a shafin na sa, har gida wadannan miyagun suka je, suka aukawa Fatuhu Mohammed, a lokacin ido na ganin ido.

Hadimin yake cewa an tasa uban gidansa a gaba domin ya gagari abokan adawarsa, har sai da ta kai sun kauce hanya wajen hana shi yin takara.

Kara karanta wannan

Bana Wasa Da Jin Dadin Iyalina Ko Kadan Kuma Ina Shirin Rufe Kofa Da ta Hudu, Lakcara mai yara 18

Da yake bayani a dandalin sada zumuntan na zamani, Ganga ya koka a game da yadda wasu ‘yan siyasa ke neman kawo cibaya a siyasar Daura.

'Dan Majalisar Daura
Hon. Fatuhu Mohammed a wajen taron mazaba Hoto: @ahmad.ganga.545
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahmad Ganga ya yi magana

“Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un. Yanzu nan miyagu suka kai wa Hon Fatuhu Muhammed hari a gidansa da yamma.
Ba su iya doke shi a filin zabe ba, sai da suka yi amfani da sojoji da sauran hanyoyin da suka sabawa dokar kasa.
Yanzu suna so su hallaka shi. Ba za a wanye lafiya ba. Siyasa ta lalace a Daura da zuwar masu neman mulki ido rufe."

A karshe ya karasa maganarsa da addu’a; Hasbunallahu wani'imal wakil, ma’ana Ubangiji Ya isa.

Jami'an tsaro su dauki mataki

An dai yi dace wadanda suka yi wannan nufi ba su yi nasara ba. Tun lokacin da wannan abin ya faru, Legit.ng Hausa ba ta ji jami’an tsaro sun ce uffan ba.

Kara karanta wannan

Fuskokin Wasu Daga Cikin Mutanen Da Yan Bindiga Suka Sace A Sabon Harin Kaduna

Daga baya Ganga ya fallasa wasu matasa biyu da suka fito daga yankin Daura da yace sun yi farin-ciki da abin, ya bada shawarar jami'an tsaro su yi ram da su.

Sanata ya shiga uku

Ku na da labari Lauyoyin Ingila suna zargin Beatrice Ekweremadu da kitsa fita da wani yaro zuwa Landan domin a cire kodarsa ba tare da ya amince ba.

Tim Probert-Wood ya kuma fadawa kotu laifuffukan da ke wuyan mai gidanta, Ike Ekweremadu, a karshe Alkali bai amince a ba Sanatan Najeriyan beli ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel