Najeriya tana da Shugaba Rago Wanda Bashi Da Kulawa - Odinkalu

Najeriya tana da Shugaba Rago Wanda Bashi Da Kulawa - Odinkalu

  • Tsohon Shugaban Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Najeriya, Farfesa Chidi Odinkalu ya ce shugaba Buhari rago ne wanda bashi da kula
  • Farfesa Odinkalu ya ce abin takaici ne yadda Buhari ya je kasar Laberiya don yin magana kan tsaro yayin da ya bar kasar babu tsaro.
  • Odinkalu ya ce gwamnoni ba su da alhakin matsalar tsaro da kasar ke fuskanta saboda ba su da hurumin ba hafsoshin Jami'an tsaro umarni

Abuja - Tsohon Shugaban Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Najeriya, Farfesa Chidi Odinkalu, ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin "Shugaba Rago kuma Mai Halin Ko'inkula ". Rahoton Daily Trust

Lauyan kare hakkin dan Adam ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan halin rashin tsaro a Najeriya a cikin shirin Sunrise Daily na Channels Television a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa tayi Martani Mai Zafi ga Sanatocin da ke Yunkurin tsige Buhari

Ya caccaki shugaba Buhari da ya fice daga kasar sa’o’i kadan bayan da wasu ‘yan ta’adda suka yi wa Dakarun Sojojin Guards Brigade kwanton bauna tare da bindige su a Abuja.

Farfesa Odinkalu ya ce abin takaici ne yadda shugaban ya je kasar Laberiya don yin magana kan tsaro yayin da ya bar kasar ba tsaro.

kALUN
Najeriya tana da Shugaba Ragon Wanda Bashi Da Kula - Odinkalu Legit.NG
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kalubalanci masu cewa gwamnonin jihohi ma suna da alhaki a matsalar tsaro da kasar ke fuskanta, inda ya ce:

"Duka hafsoshin jami’an tsaro suna karban umarnin jami’in guda daya ne kawai, kuma shine shugaban kasa.
“Idan ana maganar ‘yan sanda, sojoji, sojan ruwa, SSS, NIA, Daraktan leken asiri na soji, mai ba da shawara kan harkokin tsaro, kowanane yana kai rahoto game da tsaro zuwa ga mutum daya.
“Mukamin Shugaban kasa ba mukamin kwamanda ne kadai, shi ne shugaban gudanarwa na dukkanin wadannan hukumomin, shi kadai suke wa kai rahoto.

Kara karanta wannan

Jim kadan da Sanatoci suka yi barazanar tsige Buhari, Shugaban kasa ya dauki mataki

Chidi Odinkalu ya kara da cewa abun mamaki ne a ce an kashe jami’an Sojin Shugaban kasa a birnin Abuja sai kuma Shugaban kasar ya tafi Laberiya don gabatar da lacca akan tsaro.

Shugabanci Nagari Kadai Zai Hana Juyin Mulki – Muhammadu Buhari

A wani labari, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Talata a birnin Monrovia, kasar Laberiya, ya ce inganta dimokuradiyya da shugabanci na gari ne kadai maganin juyin mulki.

Ya kuma yi kira ga shugabannin kasashen yammacin Afirka da su yi iya kokarinsu wajen gudanar da zabe cikin aminci da gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel