Borno: Yan Boko Haram Sun Kai Wa Tawagar Shugaban Ƙaramar Hukuma Hari, Sun Kashe Ɗan Sanda

Borno: Yan Boko Haram Sun Kai Wa Tawagar Shugaban Ƙaramar Hukuma Hari, Sun Kashe Ɗan Sanda

  • Wasu yan bindiga da ake zargin yan Boko Haram ne sun kai wa jerin gwanon motocin shugaban karamar hukumar Nganzai a Borno hari
  • Mohammed Bashir Bukar, hadimin shugaban karamar hukumar Nganzai, Hon Asheikh Mamman ya ce mai gidansa lafiyarsa lau kuma ba a sace shi ba
  • Bukar, amma ya ce jami'in dan sanda guda daya daga cikin tawagar ya riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da yan ta'addan suka kai musu a hanyar su ta zuwa wani aiki

Borno - Ɗan sanda ya riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai wa tawagar motocin shugaban karamar hukumar Nganzai a Jihar Borno, Hon Asheikh Mamman Gadai, hari a ranar Laraba.

Lamarin ya faru ne a hanyar Gajiram da Gajiganna lokacin da Asheikh da tawagarsa ke hanyarsu ta zuwa wani aiki, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

An kai wa 'Dan Majalisar Daura, 'Danuwan Shugaba Buhari Hari Har Gida a Katsina

Yan ta'adda
Borno: Boko Haram Sun Kai Wa Tawagar Shugaban Ƙaramar Hukumar Hari, Sun Kashe Ɗan Sanda. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hadimin Asheikh ya tabbatar da afkuwar harin

A cikin sanarwa, Mohammed Bashir Bukar, mataimaki na musamman ga shugaban karamar hukumar Nganzai a bangaren watsa labarai ya tabbatar da harin.

Sanarwar ta ce Hon Asheikh lafiyarsa kalau, ɗan sanda cikin tawagarsa ya rasu.

An bukaci al'umma su yi watsi da jita-jitar cewa yan ta'addan sun sace Hon Asheikh.

Amma, sanarwar ba ta bada karin bayani game da harin ba. An yi kokarin ji ta bakin Bukar a lokacin hada wannan rahoton amma ba a same shi ba.

A halin yanzu dai Najeriya na fama da matsalar rashin tsaro da ake yi wa kallon mafi muni a tarihin kasar.

Dakaci karin bayani...

Asali: Legit.ng

Online view pixel