Bidiyon Rahama Sadau Tana Zuba Yaren Indiyanci, Za Ta Fito A Shirin Bollywood

Bidiyon Rahama Sadau Tana Zuba Yaren Indiyanci, Za Ta Fito A Shirin Bollywood

  • Jarumar fina-finan Kannywood Rahama Sadau ta ce tana shirin bayyana a fina-finan Bollywood na Indiya
  • Rahama ta bayyana cewa tuni suka zanta da Furodusa kuma Daraktar shirin, Hamisha Daryani Ahuja, wacce ta yi mata tayin shiga sabon fim dinta
  • Ta mika godiya ga dukka masoyanta a kan goyon baya da irin gudunmawar da suke bata wanda ya kai ta ga hawa wannan mataki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Rahama Sadau ta ce ta yiwa masoyanta albishir da cewar suna gab da fara kallonta a cikin fina-finan kasar Indiya wato Bollywood.

A wata wallafa da ta yi a shafinta na Instagram, Rahama ta bayyana cewa ta cika farin ciki bayan samun kira daga Furodusa kuma Daraktar shirin , Hamisha Daryani Ahuja cewa tana son ta fito a wani sabon fim dinta.

Kara karanta wannan

NNPC yayi karin-haske kan batun korar Ma’aikata 500 tun da kamfani ya canza tsari

Rahama Sadau
Bidiyon Rahama Sadau Tana Zuba Yaren Indiyanci, Za Ta Fito A Shirin Bollywood Hoto: rahamasadau
Asali: Instagram

Hakazalika, jarumar ta kuma wallafa wani bidiyonta tana zuba yaren Indiyanci tiryan-tiryan sai kace Ba’indiyar usuli.

Ta rubuta a shafin nata:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Na girma da kallon fina-finan Bollywood, kuma har na kan hango kaina cikin shirin a matsayin jaruma. A koda yaushe ina jin dadin yadda al’adar Indiya ke shige da al’adar da na girma a ciki.
“A lokacin da @hamishadaryaniahuja da ni muka yi magana game da yiwuwar aiki kan shirinta mai zuwa, na cika da farin ciki. Na san cewa rawar gani ne da za ta mikar da ni, sannan zai nuna kwarewata a matsayin jaruma, kuma ina zuba idon ganin abun al’ajabin da hakan zai haifar!
“Abu mafi muhimmanci, ina dokin sanar da ku dukka da kuka kamaramun baya duk daga ranar farko yadda za ta kasance. Na iya yin duk wadannan abubuwan ne, saboda kuna tare da ni.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja Za Ta Haramta Karuwanci, Wasu Mata Da Ke Harkar Sun Magantu

Kalli bidiyon a kasa:

Zafafan Hotunan Ummi Rahab Da Angonta Lilin Baba Suna Shan Soyayya

A gefe daya, Soyayya na kara karfi yayin da zama ke kara dadi tsakanin amarya kuma jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ummi Rahab da angonta kuma mawaki Shua’abu Lilin Baba.

Jarumar ta saki wasu zafafan hotunansu tare da mijin nata suna shan soyayya a shafinta na Instagram.

Sannan ta jaddada irin soyayyar da take yiwa mijin nata, tana mai alfahari da mallakarsa a matsayin abokin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel