Gwamnatin Neja Za Ta Haramta Karuwanci, Wasu Mata Da Ke Harkar Sun Magantu

Gwamnatin Neja Za Ta Haramta Karuwanci, Wasu Mata Da Ke Harkar Sun Magantu

  • Gwamnatin Jihar Neja ta ce za ta haramta karuwanci a babban birnin jihar wato Minna saboda dalilan tsaro a jihar
  • Sakatariyar Dindindin a maa'aikatar mata da ayyukan cigaba, Kaltum Rufai ne ta bayyana hakan yayin hira da ta yi da NAN
  • Wasu daga cikin masu wannan harka da aka yi hira da su sun ce rashin ayyukan yi da kuncin rayuwa yasa suka shiga harkar don su taimaki kansu

Gwamnatin Jihar Neja za ta haramta karuwanci a Minna babban birnin jihar a matsayin wani mataki na magance rashin tsaro, Daily Nigerian ta rahoto.

Kaltum Rufai, Sakataren dindindin a ma'aikatar mata da ayyukan cigaba na jihar ce ta bayyana hakan cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, a Minna.

Gwamnan Neja
Gwamnatin Jihar Neja Za Ta Haramta Karuwanci Don Dakile Rashin Tsaro. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

An Kama Mata Da Miji Saboda Lakadawa Dan Sanda 'Duka' a Legas

Ms Rufai ta ce gwamnati ta san da wannan lamarin mara dadi wanda ka iya zuzuta kallubalen tsaro da ake fama da shi a jihar.

Ta ce akwai dokoki na jihar da suka hana hakan, tana mai cewa gwamnati za ta yi bincike da nufin kawo karshen mummunan abin.

"Yanzu da kun kawo koke kan lamarin, gwamnati za ta dauki mataki.
"Da kai na zan tafi in ga sakataren gwamnatin jiha don tattauna batun da yadda za a warware shi," in ji ta.

Binciken da NAN ta yi a Minna, ya nuna cewa yan mata da mata suka fara harkar ta su ne daga karfe 7 na yamma zuwa 12 na dare.

Martanin wasu masu harkar

Wasu daga cikinsu da suka yi magana da NAN kuma suka nemi a boye sunansu sun ce su kan caji kudi daga N1,000 zuwa N10,000, bisa irin abin da ake bukata.

"Abokan huldarmu su kan biya kudin otel daga N1000 zuwa N3000 don gajerun lokaci da kuma N5000 zuwa N8000 na dare baki daya," dayansu ta fada wa NAN.

Kara karanta wannan

An samu hargitsi yayin da aka kama wasu 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangar 'yan kwadago da ASUU

Wasu daga cikinsu sun ce rashin ayyukan yi ne yasa suka shiga harkar.

Daya daga cikinsu ta ce, "dole zan yi amfani da abin da na ke da shi domin taimakon kai na."

Gwamnati Ta Fara Ƙidayar Karuwai Da Ke Zaune a Jihar Bauchi

A wani rahoton, Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce ta fara wani aikin kidaya na mako daya domin sanin adadin karuwai da ke zaune a jihar, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan dindindin, Hukumar Hisban na jihar Bauchi, Aminu Balarabe, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da kidayar karuwan, a ranar Laraba a jihar Bauchi.

A cewar PM News, Balarabe ya ce an tsara shirin ne da niyar tallafawa karuwan da kudade don su dena karuwanci, su koyi sana'o'i su zama masu dogaro da kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel