Ta Bi Shawarar Kawarta Ta Rabu Da Saurayinta Kan Cewa Ya Cika Girman Kai, Yanzu Kawar Na soyayya Da Shi

Ta Bi Shawarar Kawarta Ta Rabu Da Saurayinta Kan Cewa Ya Cika Girman Kai, Yanzu Kawar Na soyayya Da Shi

  • Wata budurwa yar Najeriya ta koka a kan cin amanar da aminiyarta ta yi mata, ta kwace mata saurayinta
  • Kamar yadda budurwar mai suna Ugochi ta bayyana, tun farko kawar ce ta shawarceta a kan ta rabu da saurayin cewa ya cika girman kai da takama
  • Kawai ta tafi hutu ne sai gashi ta dawo ta tarar da aminiyar tata tana zuba soyayya da shi saurayin nata

Wata matashiyar ‘yan Najeriya mai suna Ugochi ta hadu da cin amana mafi muni bayan kawarta ta fara soyayya da saurayinta.

Tun farko dai kawar Ugochi din ita ta shawarceta da ta rabu da saurayin nata domin a cewarta ya cika takama da izza. Ita kuma sai ta bi shawarar wajen rabuwa da shi.

Kara karanta wannan

Duk Da Kudaden Da Nake Turowa Daga Turai, Matashiya Ta Koka Da Ganin Yanayin Danta A Bidiyo

Cin amana
Ta Bi Shawarar Kawarta Ta Rabu Da Saurayinta Kan Cewa Ya Cika Girman Kai, Yanzu Kawar Na soyayya Da Shi Hoto: Twitter/@Ugochifine/nordicalagos.org
Asali: UGC

Ugochi ta je shafinta na Twitter don bayar da labarin wannan cin amana mafi girma da aka yi mata.

Ta rubuta a shafin nata:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Wannan kyakkyawan gayen yana ta bibiyata kuma yana ta yin iya kokarinsa don ganin ya ja hankalina amma sai aminiyata ta fada mani cewa na share shi saboda ya cika girman kai da izza. Duk da cewar na fada mata yadda nake son shi, sai da ta tabbatar na rabu da shi, kawai sai na dawo daga hutu naga cewa suna soyayya.
“Wasu mutanen sun daura laifin a kaina kuma na fahimci cewa na yi wauta.”

Duk Da Kudaden Da Nake Turowa Daga Turai, Matashiya Ta Koka Da Ganin Yanayin Danta A Bidiyo

A wani labarin, wata matashiya ta koka a shafin soshiyal midiya bayan ta dawo gida daga Turai ta tarar da danta cikin wani yanayi mara kyan gani.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yadda matar aure tayi mutuwar farat daya a ƙuryar ɗakin kishiyarta

Da take wallafa bidiyon yaron a shafinta na TikTok mai suna @.its_me_honey, matashiyar ta rubuta cewa tana aiki tukuru a kasar waje.

Ta kara da cewar ta tura dukka kudadenta gida don a kula mata da yaron yadda ya kamata, don haka yanayin da ta riske shi ya raunana mata zuciya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel