‘Yan Sandan Gombe Sun Kama Barayin Shanu tare da Kwato Bindigogi a Hannun su

‘Yan Sandan Gombe Sun Kama Barayin Shanu tare da Kwato Bindigogi a Hannun su

  • Yan sandan Gombe sun kama barayin shanu 12 tare da yara kanana shida a karamar hukumar Billiri
  • Kwamishinan Yansandan Jihar Gombe ya ce an samu nasarar cafke barayin shanu a jihar Gombe ne ta wasu sahihan rahoto da aka samu game da ayyukan yan fashi a yankin
  • Kwamishinan Yada Labarai, Meshack Lauco, ya ce jihar Gombe za ta ci gaba da hada kai da sauran jihohi, hukumomin tsaro domin samun zaman lafiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Gombe - Akalla barayin shanu 12 tare da yara kanana shida ne rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta gurfanar da su a yau Litinin. Rahoton PUNCH

Legit.NG ta samu rahoton cewa, an kwato shanu 483, tumaki da raguna 186, jakuna uku, babura hudu, wayoyin hannu tara, da kudi N994,000 daga hannun wadanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Miyagu sun Bindige Hadimin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Har Lahira

Da yake gabatar da wadanda ake zargin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe, Ishola Babaita, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a karamar hukumar Billiri, bayan wasu sahihan rahoton da aka samu daga majiyoyi kan ayyukan ‘yan fashin da suka addabi jihohin dake makwabtaka da su.

gombe
‘Yan sandan Gombe sun kama barayin shanu tare da kwato bindigogi a hannun su FOTO Legit.NG
Asali: UGC

Babaita ya bayyana cewa tare da hadin gwiwan jami’an sa, ‘yan banga da mafarauta suka samu nasarar kama barayin a yayin da suke hanyar su zuwa wani waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, daga cikin abubuwan da aka kwato sun hada da bindigogi kirar AK-47 guda biyu, AK-49, harsashi 320, mujallar harsashi 14, kwalabe uku da zunzurutun kudi N994,000.

Shima da yake nasa jawabin kwamishinan tsaro na cikin gida, Adamu Kupto ya bayyana cewa ana kokarin fara tantance dabbobin domin sanin hakikanin masu shi.

A nasa bangaren, Kwamishinan Yada Labarai, Meshack Lauco, ya ce jihar za ta ci gaba da hada kai da sauran jihohi, hukumomin tsaro domin samun zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-Rufai A Sabon Bidiyo

Lauco ya ce:

“Mun samu nasarar hakan ne bisa goyon bayan da gwamnan ya ba hukumomin tsaro. Idan ba don matsayin gwamna kan zaman lafiya da tsaro ba, da ba mu samu wannan ba."

Bayan barazanar garkuwa da El-Rufai, 'yan ta'adda sun kai harin ban mamaki a Kaduna

A wani labari Kuma, Yan ta'adda sun sake kai mummunan farmaki Millennium City dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da mazauna yankin.

A safiyar Talata, SaharaReporters ta gano cewa maharan sun kutsa yankin a daren Litinin inda suka kwashe sa'o'i suna aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel