Ana Kukan Babu Kudi, Gwamnatin Buhari Za Ta Kashe N30.2bn a Gyaran Majalisa

Ana Kukan Babu Kudi, Gwamnatin Buhari Za Ta Kashe N30.2bn a Gyaran Majalisa

  • Gwamnatin Najeriya ta hakikance a kan ware fiye da Naira Biliyan 30 domin a gyara Majalisa
  • Ministan birnin Abuja, Musa Mohammad Bello ya ce an fara wannan aiki, za a gama a 2023
  • Ministan ya bayyana a gaban kwamitin Sanatoci, ya shaida masu inda aka kwana a ayyukan

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce gyare-gyaren da za ayi a majalisar Najeriya zai ci Naira Biliyan 30.2. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.

Ministan harkokin birnin tarayya Abuja, Musa Mohammad Bello, ya shaidawa manema labarai irin kudin da wannan aiki zai lakume.

Naira Biliyan 37 aka ware a kasafin kudin 2020 domin gyara majalisa, amma daga baya dole aka rage kudin zuwa Naira biliyan 9.25 a tsakiyar shekara.

Musa Mohammad Bello ya sanar da kwamitin majalisar dattawa cewa asalin kudin aikin shi ne Naiara biliyan 30.2, an biya ‘yan kwangila Naira biliyan 9.2.

Ministan ya fadawa Sanatoci cewa a ranar 15 ga watan Agustan 2023 za a kammala wannan aiki da aka fara tun a ranar 16 ga watan Afrilun shekarar nan.

Rabon majalisa da gyara tun 1999

An yi wa wannan gyara da aka dauko lakabi da aikin “The White House”. Sama da shekaru 20 kenan aka shafe ba tare da an yi wa ginin majalisar gyara ba.

Majalisa
'Yan Majalisa yayin da ake wani zama Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Jaridar ta ce Mai girma Ministan ya jero aikin yi wa majalisar tarayyan kwaskwarima a cikin muhimman kwangilolin da ake yi a birnin na Abuja.

Sauran ayyukan da ake yi

Baya ga wannan aiki, gwamnati mai-ci ta na gyaran sakatariyar ma’aikatar tarayya, da kuma ginin titin southern park zuwa cibiyar Kiristoci da ke babban birnin.

Sauran muhimman ayyukan da ake kan yi sun hada da fadada hanyar Outer Southern Expressway.

Kamar yadda Ministan yake bayani, karancin kudi ya sa dole sai dai aka zabi ayyukan da aka fi bukata a daidai wannan lokaci, domin a bada kwangilarsu.

Gwamnati ta duba yawan mutanen da za su amfana ne wajen zaben aiki a matsayin muhimmi. Sanata Tolu Odebiyi shi ne shugaban kwamitin a majalisa.

Sowore da Atiku da Obi

An fitar da rahoto cewa Atiku Abubakar da Peter Obi sun ji babu dadi da suka ci karo a Twitter da Yele Sowore mai neman takarar shugaban kasa a AAC.

Mai neman takarar a jam'iyyar African Action Congress ya ragargaji Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi ne da suka yi maganar lalacewar lantarki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel