Ta'addanci na karuwa, 'yan sanda sun kama mutane 198 da ake zargin 'yan ta'adda ne a Kano

Ta'addanci na karuwa, 'yan sanda sun kama mutane 198 da ake zargin 'yan ta'adda ne a Kano

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana kame wasu mutum 198 da ake zargin 'yan ta'adda ne
  • An gurfanar da wasu daga cikin 'yan ta'addan da aka kama a ayyukan sintiri daban-daban na jami'an tsaro
  • Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na daga cikin yankunan da ke fama da matsanancin rashin tsaro a Najeriya

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane 198 da ake zargi da aikata laifuka a jihar a tsakanin 27 ga watan Yuni zuwa 20 ga watan Yuli, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Samaila Dikko ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai kan nasarorin da rundunar ta samu a ranar Alhamis a Kano.

Yadda aka kama 'yan ta'adda a jihar Kano
Karuwar ta'addanci: 'Yan sanda sun kama mutane 198 da ake zargin 'yan ta'adda ne | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya ce 42 daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne da laifin fashi da makami, tara kuma da laifin garkuwa da mutane, 16 da laifin damfara da kuma 27 masu satar motoci da masu satar babura uku.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An yi mummunan hadari, motoci 3 sun kama da wuta, mutum 30 sun kone a hanyar Zaria zuwa Kano

Sauran wadanda ake zargin sun hada da 12 da ke safarar miyagun kwayoyi, da kuma tsageru 92 da aka fi sani da “Yan daba”.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda aka kama su

Kwamishinan ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne daga sassa daban-daban na jihar a ayyukan hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro, 'yan sa kai da kai samame a maboyar ‘yan ta’addan.

Mista Dikko ya kara da cewa an gurfanar da wasu daga cikin wadanda ake zargin a kotu.

A cewarsa, ‘yan sanda sun kubutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su a lokacin da ake gudanar da aikin binciken.

Ya ce kayayyakin da aka samu daga hannun wadanda ake zargin sun hada da bindigu 25 da suka hada da AK-47 uku, motoci 12, keke napep guda bakwai, babura uku da kuma wukake 122.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan ta'adda sun shigo Kano, an sake kama mota makare da bama-bamai

Sauran kayayyakin sun hada da busassun ganye guda 269 da ake zargin tabar wiwi ne, wayoyin hannu 134, kwamfutar tafi-da-gidanka guda hudu, talabijin Plasma 16 da kayayakin bugarwa da dai sauransu.

Kwamishinan ya yabawa sauran hukumomin tsaro da kafafen yada labarai da kungiyoyin farar hula da masu ruwa da tsaki da ke taimakawa ayyukan ‘yan sanda a jihar.

Jaridar Tribune ta ba da lambobin wayan hukumar 'yan sanda da za akira idan aka samu wasu bayanan tsaro; 08032419754, 08123821575, 08076091271 ko a sauke mahnyar "NPF Rescue Me" a sahar Play Store.

Tashin hankali, 'yan bindiga sun farmaki mazauna a jihar Neja

A wani labarin, a safiyar yau Alhamis ne ‘yan ta’adda suka mamaye wasu al’ummomin yankin Kamapani Waya a karamar hukumar Kontagora a jihar Neja.

Wakilin The Nation, wanda ke kan hanyar zuwa Kontagora daga Minna a motar haya, ya koma da baya bayan ya bar yankin Kampani Waya.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Sake Kama Wasu Da Suka Tsere Daga Kurkukun Kuje A Jihohin Arewa 2

Wasu motoci ne suka sanar da direban motar cewa, akwai 'yan bindiga da ke barna kan mutanen kauyen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel