Yanzu-Yanzu: Tashin hankali, 'yan bindiga sun farmaki mazauna a jihar Neja

Yanzu-Yanzu: Tashin hankali, 'yan bindiga sun farmaki mazauna a jihar Neja

  • Rahoto daga majiya mai tushe ya bayyana yadda 'yan bindiga suka farmaki wani kauye a yankin jihar Neja
  • An ga mazauna yankin da lamarin ya shafa suna gudun tsira, tare da boye shanunsu daga sacewar 'yan bindiga
  • Ana yawan samun hare-hare a yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya, lamarin da ya raba jama'a da gidajensu

Kontagora, jihar Neja - A safiyar yau Alhamis ne ‘yan ta’adda suka mamaye wasu al’ummomin yankin Kamapani Waya a karamar hukumar Kontagora a jihar Neja.

Wakilin The Nation, wanda ke kan hanyar zuwa Kontagora daga Minna a motar haya, ya koma da baya bayan ya bar yankin Kampani Waya.

Yadda 'yan bindiga suka kawo firgici a Neja
Yanzu-Yanzu: Tashin hankali, 'yan bindiga sun farmaki mazauna a jihar Neja | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wasu motoci ne suka sanar da direban motar cewa, akwai 'yan bindiga da ke barna kan mutanen kauyen.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

Rahoton jaridar ya ce, mutanen da ke motar sai da suka koma Kampani Waya kana suka zauna a can na kusan mintuna 40.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ga mutanen kauyen cikin shiri yayin da wasu ke kira ga mata da yara su je su buya. Hakazalika, wasu sun kwashe shanunsu domin boyesu.

Duk motocin da suka taho daga Minna sai da suka tsaya don gudun shiga cikin tashin hankalin da 'yan bindigan ka iya jefa su.

A bangare guda, jaridar ta yada bidiyon lokacin da motoci ke barin hanyar bayan samun labarin 'yadda 'yan ta'addan da ke barna a yankin na jihar Neja.

Kalli bidiyon:

Wani shugaban APC ya yi ta maza, ya tsere daga hannun 'yan bindiga

A wani labarin, shugaban jam’iyyar APC gunduma ta 9 a karamar hukumar Orhionmwon ta jihar Edo, Mista Godwin Aigbogun, ya kubuta daga maboyar wadanda suka sace shi.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da jami'an yan sanda 10 a jihar arewa

Masu garkuwa da mutanen da ake zargin Fulani makiyaya ne, an ce sun bukaci iyalansa da su biya Naira miliyan 5, bayan da aka yi garkuwa da shi a hanyarsa ta komawa kauyensu daga gonarsa da ke Ologbo-nugu a yammacin ranar Litinin.

Sakataren Yada Labarai na Jihar Barista Peter Uwadiae, ya tabbatar wa da jaridar Punch cewa jigon ya tsere ne da safiyar Laraba kuma ya ce tuni ya koma ga iyalansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel