Wani mutum ya kashe budurwar sa a Delta saboda ta fasa mishi wayar iPhone 11 ProMax

Wani mutum ya kashe budurwar sa a Delta saboda ta fasa mishi wayar iPhone 11 ProMax

  • Fushi yasa wani matashi ya kashe budurwar sa a jihar Delta saboda ta fasa masa sikirin din iPhone 11 Pro Max
  • Bincike ya nuna Godspower Adigheti da Gift Oluko suna zama gida daya kamar ma’aurata kuma suna da diya mace
  • Rundunar yansandan jihar Delta ta ce Godspower Adigheti ya yi amfani da adda ya kashe Gift har lahira

Jihar Delta - Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta kama wani matashi dan shekara 23 mai suna Godspower Adigheti bisa zargin kashe budurwar sa, Gift Oloku har lahira kamar yadda PUNCH Metro rawaito

PUNCH Metro ta tattaro cewa Adigheti ya kashe Oloku, daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Delta, Ozoro, saboda lalata masa wayar iPhone 11 Pro Max da tayi.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 16 ga Yuli, 2022, a Ozoro, cikin karamar hukumar Isoko ta Arewa.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Bidiyon mutuwar amarya ana tsaka da liyafar aurenta a jikin angonta

Godspowers
Wani mutum ya kashe budurwar sa a Delta saboda ta fasa mishi wayar iPhone : FOTO Exola Tv
Asali: UGC

Wakilin PUNCH Metro ya gano cewa, Adigheti da budurwarsa sun samu sabani ne, wanda ya yi sanadin barkewar rikici a tsakanin su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wata majiya ta ce Adigheti da Gift suna zama gida daya kamar ma’aurata kuma suna da diya mace.

Ya ce:

“Gift ta fita taje unguwa, bayan ta dawo gida, sai saurayin ya nemi yaji inda taje suna cikin haka sai suka fara rigima wanda ya janyo ta fasa mai sikirin din iPhone 11 Pro Max din sa.
“Haka ya janyo saurayin ya fusata ya sareta da adda.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce:

“A ranar 16 ga watan Yuli, 2022, jami’in ‘yan sanda mai kula da Ozoro, ya samu kiran waya cewa wani Godspower Adigheti mai shekaru 23 a unguwar Oramudu, ya yanka budurwar sa mai shekaru 22 mai suna Gift Oloku da adda.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya sace janareto da lasifikar Masallaci a Adamawa, ya sheke kudin a tabar wiwi

"An kai matar asibiti inda aka tabbatar da rasuwar ta. A halin yanzu, wanda ake zargin yana tsare kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin.

An Kashe Daya Daga Cikin Limaman Katolika Biyu Da Aka Sace A Kaduna

A wani labari kuma, Masu garkuwa da mutane sun kashe Reverend Fada John Cheitnum, daya daga cikin limaman cocin Katolika guda biyu da aka sace a karamar hukumar Lere (LGA) ta jihar Kaduna. Rahoton Channels

Wanda aka kashe, shi ne Daraktan Sadarwa na cocin Katolika reshen Kafanchan, da kuma Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a karamar hukumar Jema’a ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel