An Kashe Daya Daga Cikin Limaman Katolika Biyu Da Aka Sace A Kaduna

An Kashe Daya Daga Cikin Limaman Katolika Biyu Da Aka Sace A Kaduna

  • Masu garkuwa da mutane sun kashe daya daga cikin limaman cocin Katolika guda biyu da suka sace a karamar hukumar Lere
  • Reverend Fada John Cheitnum shine shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN reshen Kafanchan
  • Baray sun sako dayan Raveren Fada Cleopas bayan an biya su makudan kudade da ba bayyana adadin su ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kaduna - Masu garkuwa da mutane sun kashe Reverend Fada John Cheitnum, daya daga cikin limaman cocin Katolika guda biyu da aka sace a karamar hukumar Lere (LGA) ta jihar Kaduna. Rahoton Channels

Wanda aka kashe, shi ne Daraktan Sadarwa na cocin Katolika reshen Kafanchan, da kuma Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a karamar hukumar Jema’a ta jihar.

A ranar 16 ga watan Yuli ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Reverend Fada Cheitnum da abokin aikinsa Reverend Fada Donatus Cleopas a lokacin da suke aikin a cocin Christ the King Catholic Church, Yadin Garu a karamar hukumar Lere.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kutsa Gonar Tsohon Gwamna a Najeriya, Sun Sace Mai Kula Da Gonar

father
An Kashe Daya Daga Cikin Limaman Katolika Biyu Da Aka Sace A Kaduna FOTO Channels
Asali: UGC

A cewar wata sanarwa da shugaban Jami’an darikar cocin Katolika na Kafanchan, Revrend Fada Emmanuel Okolo, ya ce an gano gawar limamin cocin ne a ranar Talata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Game da Reverend Fada Cleopas, an ce barayin sun sako shi ne bayan an biya su makudan kudade da ba a bayyana adadinsu ba a matsayin kudin fansa.

A ‘yan kwanakin nan, Jihar Kaduna ta sha fama da matsalar sace-sacen jama’a da dama, wanda akasari ana kai wa malaman addini hari ne.

Mun san inda aka yi garkuwa da ’yan uwan tsohon gwamnan Bauchi – ‘Yan sanda

A wani labari kuma, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi CP Umar Mamman Sanda ya bayyana cewa ‘yan sanda sun san inda ‘yan uwan tsohon gwamnan jihar Bauchi Ahmed Adamu Mu’azu suke, inda ya kara da cewa ‘yan fashin na neman naira miliyan 600 kafin su sake su. Rahoton Daily Trust

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda sun cafke wasu Malamai saboda sun yi korafi a kan Shugaban NARICT

CP Sanda ya bayyana haka ne jiya a kauyen Boto lokacin da ya raka gwamna Bala Mohammed Abdulkadir domin jajantawa iyalan tsohon gwamnan da al’ummar karamar hukumar Tafawa Balewa kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel