Saboda rashin albashi, Malamin Kwalejin Kimiya ya zama yaron bas
- Malami a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaftin Elechi Amadi da ke Fatakwal, ya zama kwandasta saboda rashin biyan sa albashi
- Hukumar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaftin Elechi Amadita ta zargi, Mista Zoe Tamunotonye da laifin yin lalata da daliba mai matakin digiri na 2
- Faifan bidiyo dake yawo a yanan gizo ya nuna Tamunotonye yana loda fasinjoji a cikin bas yana kiran wuraren da za a je
Jihar Ribas - Malami a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaftin Elechi Amadi da ke Fatakwal, Zoe Tamunotonye, ya koma yaron motar bas don tsira saboda zargin kin biyansa albashin da hukumar makarantar ta ki yi na tsawon watanni shida. Rahoton LEADERSHIP
A wata sanarwa dauke da sa hannun Rajistran makarantar, Chris Woke yace Kwalejin ta nesanta kanta daga zargin da ake yiwa Tamunotonye, na yin lalata da wata daliba mai matakin digiri 200.
Wanda sakamakon haka ta yanke masa hukuncin dakatar da shi na tsawon watanni uku, har sai an kammala bincike.
Amma an hango Tamunotonye a cikin faifan bidiyo yana loda fasinjoji a cikin bas yana kiran wuraren da za a je.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ganshi sanye da bakar wando da farar riga yana sanar da inda motar zata nufa.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na kwalejin, Benson Wekere, ya tabbatar da cewa ya ga bidiyon Tamunotonye yana yawo a yanar gizo yana aiki a matsayin kwandastan bas.
Wekere, ya ce ya sanar da mahukuntan makarantar game da lamarin amma yana jiran izini kafin ya yi magana kan batun.
Ya ce ;
“Ba zan iya yin magana a madadin kwalejin ba sai an ba ni izinin yin hakan. Abin da aka ce in fada shi ne abin da zan fada.
Karin Bayani: 'Babu Gudu Babu Ja Da Baya' ASUU Ta Dora Wa Ministan Kwadago Laifin Tsawaita Yajin Aiki
Zaben Jihar Osun: 'Mun rungumi ƙaddara' - Adamu Abdullahi
A wani labari kuma, Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Senata Abdullahi Adamu, ya ca faduwar APC a zaben gwamnan jihar Osun jarrrabawa ce daga Allah. Rahoton BBC
Abdullahi Adamu ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da BBC HAUSA, inda yace:
Asali: Legit.ng