Zaben Jihar Osun: 'Mun rungumi ƙaddara' - Adamu Abdullahi

Zaben Jihar Osun: 'Mun rungumi ƙaddara' - Adamu Abdullahi

  • Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Senata Abdullahi Adamu, ya ce faduwar APC a zaben gwamnan jihar Osun jarrrabawa ce daga Allah.
  • Abdullahi Adamu ya ce ba rashin iya siyasa bane ya janyo APC ta fadi a zaben gwamnan jihar Osun
  • Jam'iyyar APC ta yi kira ga mambobinta da su gyara kurakuran su gabanin babban zabe mai zuwa a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Senata Abdullahi Adamu, ya ce faduwar APC a zaben gwamnan jihar Osun jarrrabawa ce daga Allah. Rahoton BBC

Abdullahi Adamu ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da BBC HAUSA, inda yace

“Ya zama dole mambobin jam’iyyar APC su gyara kurakuran su gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
"Zaben Osun ya nuna mana cewa akwai aiki a gabanmu, dole ne mu gyara abubuwan da mu ke yi ba daidai ba.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka sha ƙasa a zaɓe yayin da suka yi yunƙurin tazarce kan kujerun su a Najeriya

ADAMU
Zaben Jihar Osun : 'Mun karɓi ƙaddara' - Adamu Abdullahi FOTO BBC
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Kuma faɗuwar APC a jihar Osun ba ita ce ke nufin jam'iyyar za ta faɗi a babban zaɓen dake zuwa 2023 ba.

A cewarsa jam'iyyar za ta duba abubuwan da suka janyo APC ta faɗi zaɓen jihar Osun domin gyara saboda samun nasara a zaɓen ƙasa mai zuwa.

"Harkar siyasa kamar sauran harkokin rayuwa ne, wata rana ka samu wata rana kuma ka rasa. Iko ne na Allah, babu yadda muka iya dole mu dauki kaddara.

Abdullahi Adamu ya ce ba an kayar da APC bane saboda rashin iya siyasa, sai dai matsalolin dake tsakanin 'yayan jam'iyyar gabanin zaɓen.

Kungiyar CAN ta yi korafi akan yawan sace-sacen Mambobinta a Najeriya

A wani labari kuma, Kungiyar Kristocin Najeriya CAN, ta bayyana bakicin ciki da damuwa akan yadda sace Fastocin da mabiyan su ya zama ruwan dare a jihar Kaduna da wasu sassar Najeriya. Rahoton BBC

Jagoran kungiyar CAN reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab, ya bayyana haka da yake tattaunawa da waikilan BBC, Inda ya ce :

Asali: Legit.ng

Online view pixel