Hotunan tsohuwar matar gwamna tare da kyakyawan matashi sharaf da tayi wuff da shi

Hotunan tsohuwar matar gwamna tare da kyakyawan matashi sharaf da tayi wuff da shi

  • Kyawawan hotunan tsohuwar matar marigayin gwamna da matashin da tayi wuff da shi sun matukar kayatar da masu kallo
  • Hajiya Hauwa, tsohuwar matar marigayi tsohon gwamnan jihar Taraba, Danbaba Suntai wacce tayi wuff da matashin bayan shekaru 2 da mutuwar mijinta
  • A hotunan da suka bayyana, alamu na nuna ana cin soyayya mai dadi tsakanin Hajiyar mai shekaru sama da 50 da matashin mai shekaru sama da 30

Hajiya Hauwa, tsohuwar matar marigayi tsohon gwamnan jihar Taraba, Danbaba Suntai, ta bayyana a kyawawan hotuna tare da matashin da tayi wuf da shi, Halliru Saad Malami.

Mai daukar hoto Nexus ne ya zuba hotunan a shafinsa na Instagram a ranar Talata, 12 ga watan Yulin 2022.

Hotuna
Hotunan tsohuwar matar gwamna tare da kyakyawan matashi sharaf da tayi wuff da shi. Hoto daga photosby_nexus
Asali: Instagram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau

Hajiya Hauwa ta auri Malami, wanda shine CEO na ITBAN Global Resources Ltd a shekarar 2019, shekaru biyu bayan mutuwar Suntai.

Hauwa wacce ke cikin shekarunta na 50 yayin da Malami ke shekarunsa na 30, 'dan uwa ne ga Turai Yar'Adua, matar marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar'Adua.

Idan za a tuna, wani mummunan hatsarin jirgin sama ya ritsa da Suntai a Yola a shekarar 2012 kuma an garzaya da shi kasar waje domin neman lafiyarsa.

Ya rasu a ranar 28 ga watan Yunin 2017 a Houston dake Texas, kasar Amurka, bayan gwagwarmaya da yayi da illar hatsarin jirgin saman tayi masa wacce tasa baya iya aiwatar da komai da jikinsa.

Ga hotunan a kasa:

Kyawawan hotunan gwamnan Zamfara da zuka-zukan 'ya'yansa mata 14 reras

A wani labari na daban, hotunan wankan sallar Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle tare da iyalinsa sun matukar birge jama'a.

Kara karanta wannan

Kyawawan hotunan gwamnan Zamfara da zuka-zukan 'ya'yansa mata 14 reras

A wannan hotunan, gwamnan ne tsaye tareda dukkan 'ya'yansa mata 14 reras gwanin sha'awa.

A shekarar 2019, gwamnan jihar Zamfara ya aurar da diyarsa mace daya mai suna Rukayya.

Gwamna Matawalle ya mallaki matan aure hudu, akwai Aisha uwargidansa, Bilkisu ce ta biyu, Fatima ta uku yayin da Dadiya ta kasance amarya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel