Kyawawan hotunan gwamnan Zamfara da zuka-zukan 'ya'yansa mata 14 reras

Kyawawan hotunan gwamnan Zamfara da zuka-zukan 'ya'yansa mata 14 reras

  • Hotunan gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Bello Muhammad Matawalle tare da kyawawan 'ya'yansa mata biyu sun bayyana
  • A hotunan, an ga gwamnan tsaye tare da 'yan mata goma sha uku yayin da ya rike wata karama wacce ita ce cikin ta sha hudu
  • Gwamna Bello Matawalle yana da matan aure hudu, Aisha uwargidansa, Balkisu na biye, sai Fatima ta uku yayin da Dadiya ta kasance amarya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Hotunan wankan sallar Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle tare da iyalinsa sun matukar birge jama'a.

A wannan hotunan, gwamnan ne tsaye tareda dukkan 'ya'yansa mata 14 reras gwanin sha'awa.

Matawalle and Daughters
Kyawawan hotunan gwamnan Zamfara da zuka-zukan 'ya'yansa mata 14. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

A shekarar 2019, gwamnan jihar Zamfara ya aurar da diyarsa mace daya mai suna Rukayya

Gwamna Matawalle ya mallaki matan aure hudu, akwai Aisha uwargidansa, Bilkisu ce ta biyu, Fatima ta uku yayin da Dadiya ta kasance amarya.

Kara karanta wannan

Wankan sallah: Hadadden hoton gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da yaransa maza

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matawalle and Daughters
Kyawawan hotunan gwamnan Zamfara da zuka-zukan 'ya'yansa mata 14. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Magidanci yayi shagalin sallarsa da matansa 3 da 'ya'ya 19, hotunansu sun janyo cece-kuce

A wani labari na daban, wani 'dan Najeriya yayi shagalin bikin sallah babba inda har ya bayyana hotunansa tare da matansa uku reras da 'ya'yansa 19.

Bawan Allah mai suna Baba Lawal, ya wallafa kyawawan hotunan ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yulin 2022 a shafinsa na Facebook.

A hotunan sun yi ankon kaya kalar kasa mai duhu yayin da matan suka saka hijabai kalar kayan mijinsu da 'ya'yansu sannan suka sanya niqabai a fuskokinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel