Yan Bindiga Sun Kashe Dan Uwan Tsohon Gwamna Adamu Mu'azu, Sun Kuma Sace Iyalansa

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Uwan Tsohon Gwamna Adamu Mu'azu, Sun Kuma Sace Iyalansa

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari gidan tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Adamu Mu'azu sun kashe dan uwansa sun sace wasu mutane uku
  • Mahaifiyar Mu'azu Danladi, mai shekaru 25 da yan bindigan suka kashe da bayyana yadda haduwarsu da karshe ta kasance
  • Kakakin yan sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya tabbatar da afkuwar lamarin ya kuma ce suna aiki tukuru don ganin sun ceto wadanda aka sace

Jihar Bauchi - An bindige wani Mu'azu Danladi, dan shekara 25, dan uwan tsohon gwamna Ahmad Adamu Mu'azu a kauyen Boto na karamar hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi.

An kashe Danladi ne a lokacin da yan bindigan suka kutsa gidan iyalan Mu'azu a safiyar ranar Laraba.

Taswirar Bauchi.
Yan Bindiga Sun Kashe Dan Uwan Tsohon Gwamna Adamu Mu'azu, Sun Kuma Sace Iyalansa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

An sace mutane uku yayin harin da ya bawa mutanen kauyen mamaki.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda Sadiq Ango ya canza kamanni bayan yin wata 3 hannun 'yan bindiga

Cikin wadanda aka sace akwai Hajiya Asmau Alhaji Adamu, kanwar tsohon gwamnan, Malama Halima Abdullahi da wani Nura.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A hira da Daily Trust ta yi da shi, Hashimu Abubakar Boto, wani shaidan gani da ido ya bayyana yadda abin ya faru.

"Yan bindigan sun taho misalin karfe 1 na dare suka wuce dakin da dan uwa na ya saba barci, suka balle kofa suka fara tambayarsa inda yaya da jikokin tsohon gwamnan suke? Sun bincika amma ba su ga kowa ba, hakan yasa suka harbe shi a kai kuma suka sace mutum uku a gidan," in ji shi.

A hira da Daily Trust, mahaifiyar marigayin, Hajiya Sa'adatu Adamu Mua'azu, ta yi magana kan haduwar ta da danta na karshe.

Matar wacce ta fashe da kuka ta ce, "Da na yana da kirki, biyayya da addini. Yana mayar da hankali kan abin da ke gabansa ne; baya fada da yan uwansa ko makwabta."

Kara karanta wannan

Wasu Maza Sanye Da Babban Riga Sun Tafi 'Yawon Sallah' Gidan Wani Attajiri Sun Sace Shi a Kogi

"Haduwar mu na karshe daren jiya ya nuna min hoton yar uwarsa da ke karatu a Uganda kuma ya tambaye ni naman sallarsa, wannan shine haduwar mu na karshe."

Auwalu Abdullahi Adamu, shugaban matasan PDP na mazabar Kardam B, wana mahaifiyarsa na cikin wadanda aka sace, ya ce yana barci a gidansa lokacin da ya ji harbin bindigan.

Umar Adamu Mu'azu, kanin tsohon gwamnan ya ce masu garkuwar sun fara zuwa dakin yayansa Abdurrashin Adamu Mu'azu, suna tunanin ya taho Sallah.

Ya ce masu garkuwar ba su tuntubi iyalansa ba kuma lambobin wadanda aka sace din a kashe.

Kakakin yan sanda na jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce rundunar tana aiki tukuru don ceto su.

Harin Gidan Yarin Kuje: Na Gargadi Aregbesola Kan Harin, Dakta Sadiq

A wani rahoton, Dakta Sadiq Amali na sashin nazarin halayar mutane a Jami'ar Tarayya ta Jigawa ya bayyana cewa ya yi hasashen za a kai hari gidan yarin Kuje a Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ba zam huta ba har sai na samar da sassauci ga yan Najeriya, Shugaba Buhari

Yayin da ya ke magana kan harin a shirin Sunrise Daily na Channels TV, Dakta Amali ya ce ya rubuta wasika ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbsola, game da yiwuwar kai harin.

Yan bindiga da ake kyautata zaton yan ta'adda ne, daruruwansu sun kai hari gidan yarin a ranar Talata da dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel