Biyu Babu: Gwamna Ya Ce Faston Da Aka Yi Wa 'Duka' Yayin Rusa Cocinsa Zai Kuma Biya Kudin Rusau

Biyu Babu: Gwamna Ya Ce Faston Da Aka Yi Wa 'Duka' Yayin Rusa Cocinsa Zai Kuma Biya Kudin Rusau

  • Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra ya ce dole Fasto Chukwuemeka Ohanaemere (Odumeje) zai biya kudin rusa masa cocinsa
  • Soludo, wanda ya yi magana a karshen mako ya ce gwamnati ta dade da umurtar faston ya rushe cocin da kansa amma ya ki
  • A cewar gwamnan, sun kashe kudade wurin aikin rushe cocin don haka idan an kammala za a tura masa jimillar kudin kuma dole ya biya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Anambra - Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra ya ce dole Prophet Chukwuemeka Ohanaemere (Odumeje) ya biya kudin rusa masa ginin cocinsa a Onitsha, rahoton Daily Trust.

Soludo, wanda ya yi magana a karshen mako, ya ce an aika wa Odumeje da wasu masu gidaje wasiku cewar su rushe su.

Cocin Odumeje
Bayan Rusa Wa Fasto Cocinsa, Gwamnati Ta Ce Dole Ya Biya Kudin Rusau. @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Peter Obi: Ba Zan Binciki Gwamnatin Buhari Ba Idan Na Zama Shugaban Kasa

A cewar gwamnan, wadanda ba su rusa gine-ginen da kansu ba za su biya gwamnati kudi saboda rusa musu da ta yi.

"Abin na cin mana kudi. An sanar da su su rushe ginin, amma suka ki. Ranar Alhamis aka fara rusau din. Ba a samu matsala ba sai wurin Fasto Odumeje, wanda a cewar rahotanni ya taho a motarsa a yanayi mara kyau ya yi kokarin kwace motar rusau din.
"Tabbas, ba za a fasa aikin jiha ba, kuma jami'an tsaro sun taka masa birki. Wannan mutumin ya halarci taro da dama da mu, kuma ya yi magana. Muna kashe kudi a aikin, kuma ya kamata a rushe su tuntuni, amma sun zabi su kure hakurin gwamnati.
"Da zarar mun gama aikin, za mu yi lissafi mu tura musu kudin da za su biya, kuma dole sai sun biya."

Soludo, an gano cewa, ya nesanta kansa da bada hakurin da aka ce ya yi ga malamin addinin.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Yadda wasu matan aure suka rasu a hadarin mota yayin da suke dawowa daga cefanen sallah

Ya kuma bayyana cewa akwai wasu cocin katolika guda biyu da za a rushe bisa tsarin gwamnatin jihar.

"Cocin katolika biyu an gina su ba bisa ka'ida ba sune St Dominic Catholic church and Our Lady Queen Catholic church," in ji shi.

Ya ce faston Our Lady Queen Catholic church yana nan lokacin da tawagar masu rusau suka isa, kuma ya basu hadin kai, kuma an yi hira da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel