Bauchi: Yadda dattijuwa mai shekaru 52 ta rasa ranta yayin kare 'danta daga 'yan bindiga

Bauchi: Yadda dattijuwa mai shekaru 52 ta rasa ranta yayin kare 'danta daga 'yan bindiga

  • Wata mata ta samu jinjina daga mutanen da suka santa da wadanda basu santa ba bayan labarin yadda ta rasa rayuwarta saboda tayi kokarin hana 'yan bindiga garkuwa da 'danta
  • Maryam Muhammad, dattijuwa mai shekaru 52 da ke zaune a Alkaleri ta jihar Bauchi, ta rasa ranta bayan tayi fito na fito da 'yan bindigan da suka yi dirar mikiya gidansu
  • Majiyoyi sun tabbatar da yadda matar suka dauki tsawon lokaci suna gwabza gumurzu bayan miyagun a kokarin harbin 'dan ta amma bindiga taki kama shi, hakan yasa suka so tafiya dashi

Alkaleri, Bauchi - Wata dattijuwa mai shekaru 52, Maryam Muhammad, ta tabbata a jaruma bayan 'yan bindiga sun aikata barzahu yayin da tayi kokarin kare rayuwar 'danta, inda hakan ya karya zuciya wadanda suka san ta da sauran jama'a da suka ji labarinta.

Kara karanta wannan

Shiroro: Buhari ya sha alwashin ceto 'yan China da aka sace, ya hukunta 'yan ta'adda

Mazauna Sabon Gari, wani yankin gundumar Pali ta karamar hukumar Alkaleri na jihar Bauchi, sun jinjinawa jarumta wata mata.

Late Maryam
Bauchi: Yadda dattijuwa mai shekaru 52 ta rasa ranta yayin kare 'danta daga 'yan bindiga. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daily Trust a ranar Lahadi ta gano yadda matar tayi karfin hali gami da yin gaba da gaba da 'yan bindigar da suka so yin garkuwa da 'danta. Sun halaka ta a yunkurin da tayi wajen dakatar dasu amma basu yi nasarar tafiya da shi ba. Sai dai sun raunata shi, inda aka garzaya da shi asibiti don neman lafiyarsa.

Yayin jajantawa tare da mazauna kauyen, gwamnan jihar, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya siffanta matar a matsayin gwarzuwar jaruma.

A cewarsa ba ta mutu a banza ba, inda ya kara da cewa mulkinsa zai tabbatar da kafa tarihi da ita yadda halayyarta za ta zama abin koyi ga saura, musamman mata.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da harin da aka kai jihar Neja

Yayin labarta yadda lamarin ya auku, 'diyar Maryam, Halima, ta ce:

"Sun auko gidanmu gami da janyo yayana, Yaya da ni muka yi kokarin kwace shi, amma mahaifiyarmu ta bude kofa ta fito, ta rikesa gam ba tare da sakinsa ba. Ta fafata dasu sosai," kamar yadda ta bayyana.

Ta kara da cewa, mahaifiyarsu ta dauko tabarya daga dakin girkinsu, inda ya rafkawa daya daga cikinsu gami da raunata hannunsa.

"Mahaifiyata tayi jarumta. Sun kai su 11 wandanda suka shigo gidanmu. Sun yi kokarin bindige 'dan uwana, amma da basu yi nasara ba sai suka yi kokarin tafiya da shi, amma mahaifiyata ta hanasu. Cikin rashin sa'a, suka harbeta a kai gami da tserewa."

Yayin zantawa da manema labarai, 'dan Maryam wanda ya bayyana sunansa da Babawuro Dan Azumi Muhammad, ya ce 'yan bindiga sun yi kokarin harbinsa amma sai dai harsashi baya kamasa.

Shugaban karamar hukumar Alkaleri, Yusuf Garba ya ce,

Kara karanta wannan

Niger: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 17, sun sace 'yan China 4 a wurin hakar ma'adanai

"Daga rahoton da muka samu, yayin da masu garkuwa da mutanen suka zo, sun yi kokarin balle kofar dakin yaron. Yayin da ya lura wasu na kokarin aukawa dakinsa, ya fito ya fafata dasu. A lokacin da mahaifiyarsa ta fito, ta tafi dakin girkinsu ta dauko tabarya ta kwadawa daya daga cikinsu, amma suka ki sakar mata yaronta.
"Sun yi kokarin harbinsa amma bindigar ba ta kama shi ba.
"Muna makokin ta. Za mu cigaba da tunawa da ita tare yi mata addu'a Ubangiji Allah ya biya ta, ya gafarta mata kuma ya jikanta. Daga Allah muke kuma gare shi za mu koma."

Asali: Legit.ng

Online view pixel