Babbar Sallah: Farashin tikitin jirgin sama ya ƙaru musamman zuwa jihohin arewa

Babbar Sallah: Farashin tikitin jirgin sama ya ƙaru musamman zuwa jihohin arewa

  • Farashin kuɗin tafiya a jirgin sama zuwa wasu biranen arewa sun tashi yayin da mutane suka fara komawa gida gabanin babbar Sallah
  • Wani bincike da aka gudanar ya nuna yadda farashin tikiti ya tashi daga Legas zuwa biranen arewa kamar Kano, Katsina, Yola da Ilorin
  • Al'ummar Musulmi a Najeriya zasu gudanar da Sallah Babba wato Sallar layya ranar Asabar 10 ga Dhul Hijjah

Yayin da al'ummar Musulmai a Najeriya ke shirin shagulgulan babbar Sallah nan da mako ɗaya, farashin tafiya a jiragen sama ya ƙaru a wasu manyan hanyoyi a faɗin Najeriya.

Kamfanonin jiragen sama na cigaba da alaƙanta alhakin ƙaruwar kuɗin tikitin kan tashin kuɗin litar Man Jirgin wanda ake kira da 'Jet A1'.

Mafi yawan hanyoyin da lamarin ya shafa na arewa ne kamar yadda binciken Daily Trust ya nuna cewa, kuɗin tafiya a jirgin sama zuwa manyan biranen arewa ya tashi duk da kukan da Fasinjoji ke yi game da hakan.

Kara karanta wannan

Hajji 2022: Wani Alhaji ɗan Najeriya ya maida makudan kuɗin da ya tsinta a jaka a Madinah

Jirgin sama.
Babbar Sallah: Farashin tikitin jirgin sama ya ƙaru musamman zuwa jihohin arewa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Alal misal, Jirgin Legas zuwa Kano na mafi yawan kamfanoni da suka haɗa da, Air Peace, Azman Air da Max Air, suna karɓan N108,000 kuɗin tikitin zuwa kaɗai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan muka duba Kamfanin jiragen sama na Air Peace, tikitinsa na Legas zuwa Kano ya kai N105,000 inda ya ƙaru kan yadda aka siyar makonni kalilan da suka shuɗe N70,000.

Hakanan kuma tikitin jirgin Air Peance na Legas zuwa birnin Ilorin ya kai N70,000 fiye da N50,000 da suka sanya a shafinsu na yanar Gizo-Gizo.

Tafiyar da ta fi kowace tsada yanzu a Jirgin sama ita ce Legas zuwa Yola a jirgin Max Air, wanda tikitin ya kai N135,000, yayin da Lagos-Sokoto ke laƙume N128,000 kuɗin zuwa kaɗai.

Har wa yau a kamfanin Max Air, Abuja-Katsina na cin N75,000, yayin da kuɗin jirgin Abuja-Kano ke tsakanin N65,000 zuwa N75,000. A ɗaya ɓangaren kuma Lagos-Maiduguri ya kai N105,000.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya magaantu kan sabon rikicin da ya ɓarke a PDP, ya faɗi matakan da suke ɗauka

Idan muka leƙa wasu kamfanonin kamar Azman Air, kuɗin jirgi daga Legas zuwa Kaduna ya kai N99,749 zuwa kawai. Arik Air kuma na karɓan N122,196 kan tikitin Legas-Sokoto yayin da na Legas-Yola ke tsakanin N101,205 zuwa N122,196 ya danganta da lokacin da kaje siya.

Meya kawo tashin kuɗin jirgin a yanzu?

Mafi yawan matafiyan da ke hawa jirgi sun nuna fushin su da tashin kuɗin tikiti duk da Kamfanonin jiragen saman sun kare kansu da cewa matuƙar suna son tsira dole su caji kuɗin da ya dace.

Shehu Wada, Daraktan kamfanin sufurin jirgen sama na Max Air, ya ce:

"Shin kun diba farashin da ake sayar da Man Jirgi? Kuna son mu cigaba da aiki? Muna kokarin sanya kuɗin da ya kamata domin mu cigaba da kasuwanci."

Wani mai sharhi kan harkokin sufurin jiragen sama, Babatunde Adeniji, a wata zantawa da jaridar ya ce tashin farashi ba a tikitin jirgin sama ne kaɗai ba.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta amince da dukkan sabbin ministocin da Buhari ya naɗa, jerin sunayen su

"Shin tikitin jirgi ne kaɗai ke tashi? Meyasa ake tsayawa kan sakamakon kaɗai kamar dai babu abinda ya haddasa shi? Me kuke tsammanin kamfanonin jirgen sama su yi?"
"Tabbas za'a samu raguwar kuɗin tafiyar shi ma amma ba makawa sai kuɗin ya tashi matuƙar kayan aiki suka cigaba da tashi."

Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa Musulman Najeriya zasu gudanar da shagulgulan babbar Sallah (Eid-El-Kabir) ranar Asabar, 9 ga watan Yuli, daidai da 10 ga watan Dhul-Hijjah.

Hakan ya biyo bayan ganin jinjirin watan Dhul-Hijjah ranar Laraba, kamar yadda fadar Sarkin Musulmi da ke Sokoto ta sanar.

A wani labarin na daban kuma Matar aure ta haɗa kai da ɗan uwanta sun sace Mijinta kan wata gardama

Asirin wata matar aure a Kwara ya tonu yayin da ta ƙulla yin garkuwa da mijinta kan wani sabani da ya shiga tsakanin su.

Matar mai suna Delu Ali, t a amsa laifinta, t a ce ta yi haka saboda rikicinta da shi game da raba wasu dabbobi a tsakanin su.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya ɓarke a PDP, Babban Jigo ya yi watsi da Atiku, yace wajibi mulki ya koma kudu a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel