Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Dattawa ta amince da sabbin Ministoci 7 da Buhari ya naɗa

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Dattawa ta amince da sabbin Ministoci 7 da Buhari ya naɗa

  • Majalisar dattawa ta kammala tantance sabbin ministocin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya aike mata
  • Shugaban majalisar dattawan, Sanata Ahmad Lawan, ya nemi kaɗa kuri'ar murya bayan gama tantancewa, baki ɗaya mambobin suka amince
  • Ana tsammanin shugaban zai ba ministocin shahadar kama aiki nan da yan kwanaki kaɗan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da baki ɗaya sabbin ministoci Bakwai da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gabatar mata, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sabbin ministocin da majalisar ta amince da su sun haɗa da, Henry Ikechukwu daga Abiya; Umana Umana daga Akwa Ibom; Ekumankama Nkama daga Ebonyi da Goodluck Opiah daga jihar Imo.

Sauran sune; Umar El-Yakub daga jihar Kano; Ademola Adegoroye daga jihar Ondo; da kuma Odum Udi daga jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Tana Tantance Ministoci 7 da Buhari ya Mika Sunayensu

Zauren majalisar dattawa.
Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Dattawa ta amince da sabbin Ministoci 7 da Buhari ya naɗa Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Majalisa ta tabbatar da naɗin sabbin ministocin ne jim kaɗan bayan kammala aikin tantance su, wanda ya kwashe awanni biyar ana yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika majalisar ta tantance mutanen ne ɗaya bayan ɗaya yayin zamanta na yau Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022.

Wasu ministocin an umarci su kai gaisuwa kawai su wuce yayin da wasu kuma suka sha rubdugun tambayoyi da suka shafi tattalin arziki, ilimi, tsaro da sauran su.

Mafi yawan sanatocin sun yi magana sosai kan ministocin musamman waɗan da suke wakiltar mazaɓar da sabbin naɗin suka fito.

Bayan kammala tantance su, Shugaban majalisa, Sanata Ahmad Lawan, ya jefa tambayar tabbatar da su, ta hanyar kaɗa kuri'ar murya, mambobin baki ɗaya suka amince da naɗin su.

Yaushe zasu karɓi rantsuwar fara aiki?

Ana tsammanin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai ba sabbin ministocin shahadar fara aiki nan da yan kwanaki kuma ya sanar da Ma'aikatun da kowanne zai rike.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai sabon kazamin hari Kaduna, sun kashe jami'an tsaro sun sace dandazon mutane

Sabbin Ministocin da shugaban ya naɗa zasu maye gurbin mambobin majalisar zartarwa da suka aje kujerunsu domin neman takara.

A wani labarin kuma babban jigon PDP Fayose ya yi watsi da Atiku, ya ce wajibi mulki ya koma kudancin Najeriya a 2023

Sabon rikici ya kunno kai a babbar jam'iyyar hamayya PDP, tsohon gwamnan Ekiti ya yi hannun riga da tsayar da ɗan arewa a 2023.

Ayodele Fayose, ya ce tsarin mulkin PDP ya tanadi tsarin karɓa-karba, wajibi bayan Buhari a yi adalci, ɗan kudu ya karɓi shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel