Asirin matar aure ya tonu, Mijinta ya fahimci ta ci amanarsa da mutane 9 a boye

Asirin matar aure ya tonu, Mijinta ya fahimci ta ci amanarsa da mutane 9 a boye

  • Wani Bawan Allah ya shiga halin ha’ula’i a sakamakon gano asirin matarsa, yana zargin cewa ta na bin wasu mazajen
  • Rahoton da ya zo daga shafin Gistlover a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni 2022 cewa asirin wannan matar aure ya tonu
  • Kamar yadda wannan mutumi ya fada, mai dakin ta shi malamar jinya ce wanda ta tafi karatu a makaranta nesa da shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A cewarsa, ya fara zargin matar ne tun lokacin da ta fara gabatar masa da uzuri da zarar ya nemi su yi kwanciyar aure.

Bayanin na sa da Gistlover suka fitar ya nuna cewa kusan shekararsa 10 da auren wannan mata, amma ta ci amanarsa.

Ko da ba mu san sunan wannan mutumi ba, amma ya bayyana cewa yana aiki ne a matsayin jami’in gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

'Zan daɗe ban manta da haɗuwar nan ba' FFK ya shiga shauƙi yayin da tsohuwar matarsa ta ziyarce su shekara 2 da rabuwa

Bangaren labarin da magidancin ya bada

“Ga labari na nan kamar haka. Na auri mai dakina a 2013, malamar asibiti ce. Ni kuma ma’aikaci da ke aiki da gwamnatin tarayya. Abubuwa sun cabe mana na wani lokaci, a 2017 sai ta fara karatun ilmin jinya, ta tafi makaranta. Da ta je karatu, sai mu ka rage yawan magana, kuma a gaskiya ni na jawo haka. Ayyuka sun yi mani yawa, ta yi ta kokarin tuntuba ta, abin ya gagara. Ba cin amanar ta nake yi ba, amma dai ina hira da wasu ‘yan mata ta waya. Sannu a hankali sai mai dakina ta gano hakan, ta tunkare su kai-tsaye ba tare da na sani ba, abin ya kai ga rigima, mu ka sasanta, na ba ta hakuri.”
“A wannan lokaci ba mu samun kwanciyar aure, har ga Allah ban san dalili ba. Wani lokaci zan dawo ofis a gajiye sosai, zan nemi in kwanta da matata, amma abin ba zai yiwu ba. Sai hakan ya nemi ya zama matsala. Abin ya nemi ya dauki wani sabon salo domin ta dauka ina lalata ne da matan banza, a kan haka sai ta daina sha’awa ta, amma Allah ya san cewa ba na lalata a waje. Na yi bakin kokari na wajen nuna mata gaskiya, amma ba ta gamsu ba, ta rika kokarin ayi watsi da maganar. Ta kammala karatu a 2018, mu ka dawo tare."

Kara karanta wannan

Fitacciyar 'yar fim: Bana zuwa coci, ni musulma ce kuma mai kishin addini na

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar aure
Wasu da suka yi aure Hoto: timesofmalta.com
Asali: UGC

Asiri ya tonu

A karshen labarin dai, wannan mutumi mai shekara 43 ya ce wata rana sai ta manta da wayar salularta da za ta je aiki, shi kuwa ya sa yaronsu ya bude wayar.

A nan ne ya gano irin badalar da mai dakinsa mai shekara 38 ta ke yi, ta na aikawa mazaje hotuna da bidiyonta, abin ya rikitar da shi domin bai so su rabu.

Kamar yadda ya fada, wata rana ya tsare matar, ya nemi ta rantse, sai ya tambaye ta a game da mazajen na ta, abin ya ba ta mamaki, nan ta shiga rusa masa kuka.

A nan ta tabbatar masa da cewa sun hadu da mutumin ne a otel a Abuja, kuma ta kwanta da mazaje tara bayan komawarta makaranta lokacin ta na gidan aure.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da basaraken gargajiya a wata jiha

Wannan mutumi yana shakkar ‘ya ‘yan da suka haifa amma bai da kudin yin gwajin DNA, kuma yana tsoron kamuwa da cuta. Yanzu ya na neman shawarar mutane.

Dangote ya sauko kasa

Mun samu labari cewa Elon Musk ya samu riba sosai da kamfanin motocinsa na Tesla, sai da ya samu $14bn cikin awanni 8 a makon da ya gabata a kasar Amurka.

Ribar da Attajirin Duniyan ya samu a rana guda, ta zarce gaba daya abin da Aliko Dangote ya tara. A halin yanzu Musk ya nunka Dangote dukiya akalla sau goma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel