Mai Wakar Zazu, Portable Ya Saduda Ya Mika Kansa Hannun Yan Sanda a Ogun

Mai Wakar Zazu, Portable Ya Saduda Ya Mika Kansa Hannun Yan Sanda a Ogun

  • Fitaccen mawakin Najeriya Habib Okikiola da aka fi sani da Portable ya kai kansa ofishin yan sanda kan batun umurcin dukan wani da ya bada a bidiyo
  • Kakakin yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da cewa Portable ya kai kansa hedkwatar rundunar da ke Abeokuta a ranar Laraba
  • Oyeyemi ya ce an yi wa Portable tambayoyi yayin da ya taho tare da mahaifinsa da manajansa kuma an bada belinsa a yayin da ake cigaba da bincike

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ogun - Rundunar yan sandan Jihar Ogun, a ranar Alhamis ta bayyana cewa wanda ya yi wakar Zazu, Habib Okikiola wanda aka fi sani da Portable, ya kai kansa hedkwatar yan sanda da ke Eleweran, Abeokuta.

Idan za a iya tunawa Rundunar Yan sandan ta umurci shi ya kai kansa ofishinta mafi kusa bayan fitowar wani bidiyo inda ake zargin ya umurci wasu gungun yara su yi wa wani mutum mai suna DJ Chicken duka.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An yi dirama a majalisa, tsakanin Ahmad Lawan da Okorocha

Habib Okikiola
Mai Wakar Zazu, Portable Ya Saduda Ya Mika Kansa Hannun Yan Sanda a Ogun. Hoto: @nigeriantribune.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rundunar, ta bakin kakakinta Abimbola Oyeyemi, ta ce Portable ya kai kansa ofishinta a ranar Laraba misalin karfe 5 na yamma da mahaifinsa da manajansa, Nigerian Tribune ta rahoto.

Oyeyemi, mai mukamin DSP ya ce an masa tambayoyi a ofishin sauraron korafin al'umma bisa umurnin Kwamishinan Yan sanda, CP Lanre Bankole.

"Rundunar yan sanda tana son sanar da al'umma cewa mawaki Habib Okikiola a.k.a Portable da aka umurci ya mika kansa kan bidiyon da aka gani yana umurtar gungun samari su yi wa wani da ake kira DJ Chicken duka ya kawo kansa hedkwatan yan sanda da ke Eleweren a ranar Laraba 29 ga watan Yunin 2022.
"Mawakin ya iso misalin karfe 5 tare da mahaifinsa da manajansa. Nan take aka kai shi ofishin sauraron korafin al'umma bisa umurnin kwamishina CP Lanre Bankole, inda aka masa tambayoyi kan hannunsa cikin dukar da aka yi wa yaron a bidiyon.

Kara karanta wannan

Yadda aka Halaka Wani Mutum Saboda ya Goyi Bayan Batanci ga Annabi

"Amma, tunda laifin da aka aikata ana iya bada beli, kuma ga yajin aiki da ma'aikatan gwamnati ke yi a jihar mu da ya shafi kotu, an bada belin wanda ake zargin hannun wanda ya tsaya masa kuma ya yi alkawarin zai kawo shi duk lokacin da ake bukatarsa.
"Shima wanda aka yi wa dukkan an gayyato shi domin ya bada ba'asi daga bangarensa don bawa yan sanda damar kammala bincike kan lokaci."

Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Umurci Mawaki Portable Ya Kai Kansa Ofishinta Ko Ta Kamo Shi

Tunda farko, rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Ogun ta umurci fitaccen mawakin Najeriya, Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable ya kai kansa ofishinsu mafi kusa nan take ko kuma a kama shi.

Hakan ya biyo bayan zargin duka da aka ce ya yi wa tsohon DJ dinsa mai suna DJ Chicken, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sarkin Minna ya shiga tsakanin rikicin yan sanda da yan banga

A wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, Portable, wanda ya yi magana da harshen Yarbanci ya umurci yaransa su yi wa DJ Chicken duka kan zargin ya tura wa matarsa sako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel