Ambaliyar ruwa ta lakume rayuka, ta lalata gidaje sama da 2,000 a jihar Kano

Ambaliyar ruwa ta lakume rayuka, ta lalata gidaje sama da 2,000 a jihar Kano

  • Wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya halaka mutum uku da wasu gidaje sama da 2,000 a kananan hukumomi 5 a jihar Kano
  • Shugaban hukumar SEMA, Dakta Sale Jili, ya ce tuni hukumar ta kai ɗaukin gaggawa yankunan da abun ya shafa tare da tallafa wa mutane
  • Ya shawarci mazauna Kano su tabbatar sun yi wa ruwa hanya don guje wa faruwar makamancin haka nan gaba

Kano - Aƙalla mutum uku ne suka rasa rayukansu yayin da gidaje 2,250 suka hallaka sanadiyyar wata Ambaliya da mamakon ruwan sama a ƙananan hukumomi biyar na jihar Kano.

Shugaban hukumar kai ɗaukin gaggawa ta jihar Kano, SEMA, Dakta Sale Jili, shi ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Matar Ciyaman Din NULGE Na Jihar Zamfara Da Cikin Wata 9

Yadda ruwa ya mamaye wata Firamare.
Ambaliyar ruwa lakume rayuka, ta lalata gidaje sama da 2,000 a jihar Kano Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewarsa, ƙananan hukumomin da lamarin Ambaliyar ya shafa sune: Rano, Kibiya, Doguwa, Danbatta da kuma Kiru.

Bayan aukuwar wannan lamarin, Dakta Sale Jili, ya shawarci baki ɗaya mutanen da ke zaune a dukkan sassan Kano su samar wa ruwa hanya ta hanyar gyara hanyoyin Lambatu da ke gaban gidajen su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabinsa ya ce:

"Hukumar kula da hasashen yanayi (NiMeT) ta bayyana hasashenta na ruwan sama a daminar bana 2022, inda ta yi hasashen saukar ruwan sama mai tsanani a jihar Kano."
"Mun ɗauki matakan kai agajin gaggawa ta hanyar ziyartar dukkan yankunan da abun ya shafa don jajantawa mutanen da lamarin ya taba da kuma raba musu kayan rage radaɗi a madadin gwamnatin jiha."

Wane mataki zasu ɗauka nan gaba?

Bugu da ƙari, Dakta Saleh ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ba zata yi ƙasa a guiwa ba a kokarin da take na kare rayuka da dukiyoyin al'ummarta.

Kara karanta wannan

Dalibai 15000 za su iya rasa rubuta jarrabawar NECO a jihar Kano saboda bashin N1.5bn

"Hukumar mu ba zata runtsa ba a kokarin da take na kare rayukan al'umma da dukiyoyin su."

A wani labarin kuma Alƙalin Kotun Musulunci ya ɗage shari'ar jaruma Hadiza Gabon saboda matarsa bata da lafiya

Alƙalin Kotun Shari'ar Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna, Khadi Rilwanu Kyaudai, ya ɗage cigaba da zaman shari'ar fitacciyar jarumar Kannywood , Hadiza Gabon.

An ɗage zaman shari'ar zuwa ranar 1 ga watan Agusta, 2022, biyo bayan rashin lafiyar da matar Alƙalin ke fama da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel