Dalibai 15000 za su iya rasa rubuta jarrabawar NECO a jihar Kano saboda bashin N1.5bn

Dalibai 15000 za su iya rasa rubuta jarrabawar NECO a jihar Kano saboda bashin N1.5bn

  • Za a fara yin jarrabawar NECO na shekarar 2022, amma babu tabbacin za a zana da daliban jihar Kano
  • Hukumar jarrabawar kasar ta na bin Gwamnatin jihar Kano bashin da ya kai Naira biliyan 1.5 a yanzu
  • A dalilin wannan tulin bashi, jami’an NECO ke neman hana daliban makarantun jihar yin jarrabawa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Hukumar jarrabawa ta kasa watau NECO ta na barazanar haramtawa daliban sakandaren jihar Kano rubuta jarrabawar SSCE ta wannan shekarar.

Rahoton da ya fito daga Sahelian Times ya nuna cewa hukumar ta NECO mai shirya jarrabawa, ta na ikirarin cewa ta na bin gwamnatin Kano bashin kudi.

Kudin da ake bin gwamnatin jihar bashi na jarrabawar daliban makarantu ya kai Naira biliyan 1.5. Da wannan kudi hukumar ta ke so ta yi wasu harkokin ta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kama wanda ya harbe tsohon hadimin Jonathan, Ahmad Gulak

Idan hukumar NECO ta dauki tsauttsauran mataki, kuma gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ba ta dauki mataki ba, yara da-dama ba za su yi jarrabawa ba.

Leadership ta ce akwai ‘yan makaranta akalla 15, 000 da za su iya rasa wannan jarrabawa ta kammala karatun sakandare daga makarantun Kano a bana.

An yi haka, an biya N300m - Gwamnati

Wata majiya daga ma’aikatar ilmi ta shaidawa jaridar cewa NECO ta na bin su bashin kudi, amma ana kokarin ganin yadda za a biya wadannan kudi tun wuri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu zana NECO
Dalibai su na rubuta jarrabawa Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Kamar yadda majiyar ta bayyana, gwamnatin Kano ta biya hukumar Naira miliyan 300 a makon jiya. Ana bukatar cikon kudin domin yin wasu aikaca-aikace.

Sakatariyar din-din-din, Lauratu Ado ta ce hukumar ta kasa ta nemi gwamnati ta biya akalla Naira miliyan 700 kafin a kyale daliban Kano su zana jarrabawar.

Kara karanta wannan

A Shirye Nake In Jagoranci Yaki da 'Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan Bauchi

An sake yin abin kunya a 2022

Wannan abin kunya ya biyo bayan sabanin da aka samu tsakanin hukumar jarrabawar da gwamnatin Ganuje, aka ki fitar da sakamakon jarrabawar yara.

NECO ta hana daliban da suka fito daga jihar Kano samun sakamakonsu a shekarar da ta wuce. An dauki wannan mataki ne domin ayi maganin taurin bashi.

Kawo yanzu da aka fara jarrabawar a yau Litinin, ba mu da labarin halin da daliban suke ciki.

'Yan siyasa da shaye-shaye

An samu labarin Janar Buba Marwa mai ritaya ya ce NDLEA ta kama wasu ‘yan siyasa dauke da mugayen kwayoyi, har hukumar ta yi nasarar aika wani kurkuku.

Shugaban NDLEA ya ce su na fama da wasu matsaloli duk da irin kokarin da yake yi a ofis. Daga ciki akwai karancin wuraren horas da tsofaffin 'yan shaye-shaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel