Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda, Shaguna da Gidaje a Bukkuyum

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda, Shaguna da Gidaje a Bukkuyum

  • 'Yan ta'adda sun kai mummunan farmaki kauyen Zugu dake karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara
  • Sun kone ofishin 'yan sanda kurmus tare da tarwatsa 'yan sandan kuma sun hada da shaguna da wasu gidaje duk suka babbake
  • Kamar yadda mazauna garin suka tabbatar. wasu jama'a duk suntattara komatsansu inda suka lula gudun hijira

Bukkuyum, Zamfara - 'Yan bindiga a ranar Alhamis sun kone ofishin 'yan sanda, shaguna da gidaje uku a kauyen Zugu dake karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

Sai dai, wani shugaban matasa a Bukkuyum, Abubakar Garba, yace babu wanda aka kashe a farmakin, Premium Times ta ruwaito.

Taswirar Jihar Zamfara
Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda, Shaguna da Gidaje a Bukkuyum. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Yace bayan harin, mazauna yankin da yawa sun yi gudun hijira zuwa Bukkuyum da sauran kauyukan dake karamar hukumar Gummi ta jihar.

Zugu shine kauye na biyu a girma a karamar hukumar Bukkuyum.

Kara karanta wannan

Borno: 'Yan Ta'adda Sun Kai Mummunan Farmaki Sansanin Sojoji, Sun Yi Awon Gaba da Makamai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"'Yan bindiga daga dajin Gando sun kai farmaki. Abinda wasu mazauna garin suka sanar min cikin wadanda suka tsere zuwa Bukkuyum shi ne an kone gidaje uku dake kusa da ofishin 'yan sandan.
"Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan sun wuce tare da dawowa sannan suka kai harin.
"Abinda muka yarda shine, 'yan bindigan sun dawo Zugu ne domin halaka 'yan sanda a ofishin su dake kauyen. 'Yan bindigan sun san cewa 'yan sanda zasu amsa kiran gaggawa, hakan yasa suka yanke hukuncin kai musu hari da farko," yace.

Garba yace sun yi sata a shagunan kafin su banka musu wuta.

Yace da yawan mutane sun jigata sakamakon raunikan da suka samu na harbin bindiga yayin da wasu kuma suka samu rauni wurin kokarin tserewa.

Wani wanda harin ya ritsa da shi

"Ina Gummi lokacin da na samu kira kan cewa 'yan bindiga sun shiga Zugu kuma zasu yo yammacin yankin. Ba su kashe kowa ba amma dukkan 'yan sandan dake ofishin sun tsere kafin 'yan bindigan su isa," wani basaraken yankin yace, wanda ya bukaci a boye sunansa.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Sake Jaddada Cewa Sai An Ladabtar Da 'Yan Ta'adda, Ya kwatantasu da Ragwaye

Basaraken yace ana kula da 'yan gudun hijiran a Bukkuyum.

Mohammed Shehu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, bai daga waya ba da aka dinga kiransa domin jin yadda harin ya kasance.

Dakarun NAF Sun Dakile Yunkurin Satar Shanu, Sun Halaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa

A wani labari na daban, dakarun sojin saman Najeriya sun budewa tawaga biyu ta masu satar shanu yayin da suka kai wani samame a Jihar Zamfara da Neja wut ata jiagen yaki.

Haka zalika, dakarun, tare da soji uku na saman Najeriya (NAF), jiragen yaki da jiregen bindigu sun kai samame ga 'yan ta'addan a jihar Kaduna gami da tarwatsa sansanin su a ranar Laraba.

Wani jami'in binciken sirri na sojin, wanda ke daya daga cikin wadanda suka kai samamen Zamfara, ya bayyana yadda aka sheke 'yan ta'adda 20 a wurin Kofar Danya na jihar, yayin da suka yi yunkurin sace shanu 200.

Kara karanta wannan

An kashe akalla mutum 16 a sabon harin da aka kai jihar Benue

Asali: Legit.ng

Online view pixel