Yan Bindiga Sun Sace Mutane 22 A Yayin Da Suke Aiki A Gonakinsu a Abuja

Yan Bindiga Sun Sace Mutane 22 A Yayin Da Suke Aiki A Gonakinsu a Abuja

  • Yan bindiga sun kai hari kauyen Rafi Daji da ke iyakar birnin tarayya Abuja da Jihar Niger sun sace mutum 22
  • Wadanda suka sace din manoma ne da ke aiki a gonakinsu a yayin da yan bindigan masu yawa suka ci karfinsu suka tafi da su
  • Majiyoyi da dama sun tabbatar da sace mutanen 22 ciki har da yan sanda, mazauna garin da hakimin yankin, Alhaji Bala Mohammed

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - A kalla mutum 22 ne aka sace a wani gari da ke Abuja bayan harin da wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai.

Da ta ke tabbatar da harin, Rundunar yan sandan Abuja, a ranar Juma'a ta ce harin ya faru ne a Rafin Daji, wani gari da ke iyakar Niger da Abuja.

Kara karanta wannan

Borno: 'Yan Ta'adda Sun Kai Mummunan Farmaki Sansanin Sojoji, Sun Yi Awon Gaba da Makamai

Yan Bindiga Abuja
Yan Bindiga Sun Sace Mutane 22 A Yayin Da Suke Aiki A Gonakinsu a Abuja. Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

A cewar kakakin yan sandan Abuja, Oduniyi Omotayo, wanda ya tabbatar wa Channels Television harin ya ce yan bindigan sun kai harin yayin da manoma ke gonakinsu suna aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Manoman suna gonakinsu suna aiki yayin da yan bindigan masu yawa suka sace su," kakakin yan sandan ya rubutu cikin gajeruwar sakon WhatsApp.

Amma, Omotayo bai bada cikaken bayani game da harin ba da sunayen wadanda aka sace.

Kakakin na yan sandan ya ce an tura tawagar jamian tsaro zuwa yankin da nufin su bi sahun yan bindigan su ceto mutanen a kuma kama wanda ake zargin.

Abin da shaidun gani da ido suka ce game da harin

Shaidun gani da ido sun ce yan bindigan sun yi ta harbe-harbe a lokacin da suka kawo harin amma babu wanda ya mutu.

A cewar shaidan, maharan sun sace manoma 22, sun kona tarakta biyu mallakar manoman yankin.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun ceto wasu mutane 14 da aka yi garkuwa da su a dajin Zamfara

Akwai wasu yan gida daya su 13 da ke cikin wadanda aka sace din.

Dan uwan wasu cikin wadanda aka sace, Injiniya Ibrahim Barde ya ce kaninsa da iyalansa ba su dade da gama aiki ba sai yan bindigan suka kai harin.

Ya bada sunansu kamar haka; “Ismaila Barde, Mustapha Barde, Nasiru Barde, Abdulkarim Barde, Sanusi Barde, Usman Barde, Nura Barde, Abdullahi Barde, Babawo Barde, Farida Ayuba, Hauwa Ayuba da Husai Abdullahi.

Injiniya Barde ya ce yan bindigan sun tuntube su amma ba su fada kudin fansa ba.

A bangarensa, hakimin yankin Gurdi, Alhaji Bala Mohammed shima ya tabbatar da harin amma ya ce bai gama samun cikaken bayani ba.

Alhaji Bala ya koka kan yawaitar hare-haren da yan bindiga ke kai musu daga Abuja zuwa Niger.

Ya yi kira ga hukumomi su dauki matakan magance lamarin.

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama

A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.

Sace basaraken na zuwa ne kwanaki uku bayan sace wani kwararren masanin kimiyyan magunguna, AbdulAzeez Obajimoh, shugaban kamfanin magunguna na AZECO Pharmaceutical da ke Ozuwaya a Okene, yankin Kogi Central.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164