‘Yan sanda sun ceto wasu mutane 14 da aka yi garkuwa da su a dajin Zamfara

‘Yan sanda sun ceto wasu mutane 14 da aka yi garkuwa da su a dajin Zamfara

  • Jami'an yan sanda a jihar Zamfara sun yi nasarar ceto wasu mutane da yan bindiga suka yi garkuwa da su
  • Yan sandan da wasu jama'ar gari sun hada hannu inda suka far ma mabuyar yan ta'addan a dajin Kunchin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar
  • Sunyi aiki ne da wani bayanan sirri da suka samu a kan shige da ficen yan ta'addan, kuma mutanen da aka ceto sun yi kwanaki 42 a hannun wadanda suka sace su

Zamfara - Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa jami’anta sun ceto wasu mutane 14 a yayin wani aiki da suka gudanar a dajin Kunchin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa an yi garkuwa da mutanen ne daga garuruwansu da ke Nasarawa Wanke da Rijiya a karamar hukumar Gusau.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama

Sun shafe tsawon kwanaki 42 a tsare kafin aka ceto su a ranar Talata.

Jami'an yan sanda
‘Yan sanda sun ceto wasu mutane 14 da aka yi garkuwa da su a dajin Zamfara Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Mohammed Shehu, kakakin yan sandan jihar Zamfara, a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis, ya ce jami’an yan sanda da taimakon wasu mutane suka ceto mutanen bayan sun samu bayanan sirri game da mabuyar yan bindiga a dajin, jaridar The Guardian ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu ya ce:

“Rundunar yan sandan jihar Zamfara a kokarinta na kare rayuka da dukiyoyi a jihar, ta ceto wasu mutane 14 da aka yi garkuwa da su a yayin wani aikin ceto a dajin Kunchin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar.
“A ranar 21 ga watan Yunin 2022, jami’an yan sanda da aka tura hanyar yankin Kunchin Kalgo tare da hadin gwiwar wasu mutane da suka yanke shawarar hada kai da hukumomin tsaro don dawo da zaman lafiya jihar sun yi aiki da wasu bayanan sirri da suka samu sannan suka kai mamaya mabuyar yan bindigar, lamarin ya kai ga ceto mutane 14 ciki harda kananan yara biyu yan shekara daya.

Kara karanta wannan

An Gano Mabuyar Yan Ta'adda A Jihohin Niger Da Kwara, Majalisar Dattawar Najeriya

“A yayin zantawa da su, wadanda abun ya ritsa da su sun sanar da yan sanda cewa yan bindigar sun farmaki kauyukan Nasarawar Wanke da Rijiya a karamar hukumar Gusau sannan suka sace su zuwa mabuyarsu, inda suka shafe tsawon kwanaki 42 a tsare.
“Kwamishanan ‘yan sanda, CP Ayuba N. Elkanah a lokacin da yake mika wadanda abin ya shafa ga ‘yan uwansu, ya yabawa gwamnati da al’ummar jihar bisa ci gaba da goyon baya da hadin kai da suke ba ‘yan sanda tare da bayar da tabbacin kara zage damtse wajen ceto wadanda aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya. wadanda abin ya shafa sannan a hada su da yan uwansu.”

Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama

Mun ji cewa a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni ne wasu yan bindiga suka farmaki gidajen da ke yankin Rahamawa da Shagari low-cost a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Daya daga 'yan matan Chibok: Na san marigayi Shekau, sauran mata 20 a hannun BH

Maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna yankin da ba a san adadinsu ba, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Wata majiya a karamar hukumar Jibia wacce ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa an gano maharan da tsakar rana suna tisa keyar mutanen da suka sace zuwa inda suka ajiye baburansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel