Cikakkun Sunaye da Hotunan 'Yan Najeriya 8 da Interpol Ke Nema Ido Rufe

Cikakkun Sunaye da Hotunan 'Yan Najeriya 8 da Interpol Ke Nema Ido Rufe

  • Hukumar 'yan sandan kasa da kasa hukuma ce da tafi kowacce girma a fadin duniya mai mambobi 190 dake hada kai wajen yaki da ta'addanci
  • Kasancewar hukumar binciken mai girma ne yasa idan tana neman wani take fitar da sanarwa ga dukkan 'yan sandan fadin duniya na kasashe
  • Interpol na neman 'yan Najeriya 8 bisa tuhumarsu da ta'addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka da suka yi a wasu kasashen

'Yan sandan kasa da kasa hukumarar 'yan sanda ce da tafi kowacce girma a duniya tare da mambobi 190 - na kasashen da ke hada kai wajen magancewa gami da kawo mafita ga hatsabibanci a fadin duniya.

Idan wani mai laifi ya tsere zuwa wata kasa don gujewa gurfanarwa, 'yan sandan kasa da kasa zasu fitar da sanarwa ga dukkan 'yan sandan fadin duniya game da hatsabibin da ake nema tsakanin kasashe. Sanarwar ita ce ake bawa hukumomin shari'a na fadin duniya tare da damko mai laifin.

Kara karanta wannan

Yadda fasinjoji 18 suka kone kurmus a wani hatsari da afku a jihar Neja

'Yan Najeriya 8 da Interpol Ke Nema ido Rufe
Cikakkun Sunaye da Hotunan 'Yan Najeriya 8 da Interpol Ke Nema Ido Rufe. Hoto daga @INTERPOL_HQ
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga wasu daga cikin 'yan Najeriyan da 'yan sandan kasa da kasa ke nema ruwa a jallo kamar yadda suka bayyana;

1. Vitus Akachi

Angola na neman Vitus, wanda aka haifa a 13 ga watan Yuni 1984 ruwa a jallo bisa zarginsa da mallakar abubuwa masu fashewa ba bisa ka'ida ba, garkuwa da mutane tare da fashi da makami.

2. Salif Bouhari

Kasar Sin na neman Salif mai shekaru 59 ruwa a jallo bisa safarar miyagun kwayoyi da yake yi.

3. Nikem Butchang Timloh

Canada na tuhumar Nikem, wanda aka haifa a 25 ga watan Nuwamba 1988, tare da nemansa ruwa a jallo bisa tuhumarsa da cin zarafi ta hanyar lalata gami da kin cika sharuddan da aka gindaya masa.

4. Okromi Festus

An haifi Okromi Festus a ranar 26, 1965 kuma India ke neman sa ido rufe bisa tuhumarsa da cuta da hatsabibanci.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kwankwaso ya tabbatar da cewar suna kan tattaunawa da Peter Obi don hada gwiwar NNPP da LP

5. Costa Da Costa Frankle Austine

Wannan mutumin mai shekaru 59 ana nemansa ido rufe a kasar Indiya bisa tuhumarsa da kwafan muhimmin abu da ya shafi tsaro, mallakar takardun da aka kwafa bayan ya san ba na gaskiya bane tare kokarin amfani da su a matsayin na gaskiya da kuma kwafar sa hannu da nufin yin zamba.

6. Uzoma Eneh Jude

Brazil na neman Uzoma, wanda aka haifa a 11 ga watan Agustan 1973 bisa kama shi da laifin safarar miyagun kwayoyi.

7. Asuquo Mbuotidem Edem

Kasar Ghana na neman mutumin mai shekaru 33 'dan asalin Calabar ruwa a jallo bisa zarginsa da fashi da makami da kuma fyade.

8. Obidiozor Malahi Ikechukwu

An haifesa a ranar 30 ga watan Yuni 1979, sannan Angola na neman Malahi ido rufe bisa zarginsa da laifin garkuwa da mutane, fashi da makami da mallakar abubuwa masu fashewa ba tare da ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

Asali: Legit.ng

Online view pixel