Yanzu Yanzu: Kwankwaso ya tabbatar da cewar suna kan tattaunawa da Peter Obi don hada gwiwar NNPP da LP

Yanzu Yanzu: Kwankwaso ya tabbatar da cewar suna kan tattaunawa da Peter Obi don hada gwiwar NNPP da LP

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Kwankwaso, ya ce yana tattaunawa da takwaransa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi kan yiwuwar maja a zaben 2023
  • Kwankwaso ya ce hada gwiwarsu tana da muhimmanci musamman ganin cewa jam'iyyun APC da PDP ba su tsayar da dan takara daga jihar gabas ba
  • Sai dai ya ce babba a tsakaninsu ne zai zama shugaban kasa sannan karami ya dauki mataimakin shugaban kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabiu Kwankwaso, a ranar Asabar, ya tabbatar da cewar jam’iyyarsa na kan tattaunawa da jam’iyyar Labour Party da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi.

Ya ce suna tattaunawa ne kan yiwuwar yin maja a babban zaben shugaban kasa ta 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Peter Obi su na tsere da INEC domin yi wa PDP da APC taron dangi mai-karfi

Peter Obi and Kwankwaso
Maja tsakanin NNPP da LP: Muna kan tattaunawa da Peter Obi – Kwankwaso Hoto: Change Nigeria
Asali: UGC

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da sashin Hausa na BBC a ranar Asabar, 18 ga watan Yuni.

Kwankwaso ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A gaskiya muna tattaunawa da shi Peter Obi ko kuma ince kwamiti na aiki don ya dudduba dukkanin abun da ya kamata ya duba na aiki kuma mutane, abokai da yan uwa duk suna zuwa suna magana kuma na san shima chan ana zuwa ana yi masa magana.
"Musamman ka ga da PDP da APC yanzu basu sa koda mutum daya daga jihar gabas ba, saboda haka idan muma bamu dauka ba toh ka ga ta tabbata cewa babu wani tsari wanda za su samu ko na shugaban kasa ko na mataimakin shugaban kasa a cikin wannan tsarin wanda ta taso na 2023."

Da aka tambaye shi kan ko waye zai yi shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa a tattaunawar sai Kwankwaso ya ce:

Kara karanta wannan

Da walakin goro a miya: Jerin yan siyasa 2 da ba yan PDP da suka gana da Wike a cikin mako 1

“Toh shi ake tattaunawa amma dai ai yadda abubuwa suke tafiya, ai babba shine babba cikin tsarin kuma idan an duba an ga waye babba toh shikenan sai a zaba shi kuma karami sai ya zamana an bashi karamin.”

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa tun bayan da Obi da Kwankwaso suka kaddamar da kudirinsu na neman takara, sun samu gagarumin goyon baya daga yankuna daban-daban na kasar nan.

Legit,ng Hausa ta nemi jin ta bakin wani marubuci mai zaman kansa kan batun inda ya ce dama ana samun irin wannan tattauanwar idan aka ce guguwar zabe ta kado.

Ya ce:

"Tattaunawa irin wannan ta siyasa a gabanin zaɓe ba abin mamaki bane, kuma ba kansu farau ba, saboda tattaunawar siyasa ce ta kawo jam'iyyar APC har ta kawar da gwamnati mai ci.
"Sai dai wani hanzari ba gudu ba, kwaskwararren dokar zaɓe na shekarar 2022 ya samar da wasu tanade tanade kafin maja ta tabbata.

Kara karanta wannan

Majan LP da NNPP: Sai dai Peter ya zama mataimaki, Kwankwaso shugaba, inji NNPP

"Sashi na 81 (1) ya tanadi cewa jam'iyyu 2 ko fiye da haka zasu iya maja tare da amincewar hukumar zaɓe bayan jam'iyyun sun miƙa takardar buƙatar hakan ga hukumar. Sashi na 81 (2) kuwa cewa yayi sai kowacce jam'iyya cikin jam'iyyun dake da ƙudurin maja ta sanar da INEC gabanin babban zaɓe da watanni 9.
"Hakazakika sashi na 81 (3a) ya yi nuni da cewa buƙatar maja da jam'iyyun zasu miƙa ma INEC sai ya kasance tare da sahhalewar babban taron jam'iyyar na musamman watau Special Convention, dake tabbatar da amincewarsu da majar. Sai kuma sashi na 82 (1) ya umarci jam'iyyun su sanar da INEC shirin wannan babban taro na musamman kafin kwanaki 21. Sannan sashi na 82 (5) yace idan ba a cika sharuɗɗan nan ba maja ba zata yiwu ba.
"Idan aka lissafa, ana buƙatar aƙalla watanni 10 don samar da halastacciyar maja tsakanin jam'iyyar Kwankwaso, NNPP da jam'iyyar Peter Obi, LP.

Kara karanta wannan

Ba ku da tsari: Dan kashenin Jonathan ya fice daga PDP, ya caccaki tsarin jam'iyyar na 2023

"Sai dai, ko daga yau zuwa watan zaɓe Feburairu, bamu da watanni 9! balle 10!
"Tunda ta tabbata ƙarara maja tsakanin NNPP da LP ba zai yiwu a doron doka ba, ta wacce hanya Kwankwaso da Peter zasu yi aiki tare? Amsar ita ce sai dai idan ɗayansu zai janye takararsa kuma ya fita daga jam'iyyarsa sa'annan ya shiga jam'iyyar ɗayan, sai ya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ko na shugaban ƙasa idan masu takarar sun janye masa.
"Misali, Peter Obi ya janye takararsa a LP kuma ya fice daga cikinta, sai ya koma NNPP, yayin da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a NNPP ya janye takararsa sai a maye gurbinsa da Peter, ko kuma Kwankwaso ya yi kwatankwacin haka a LP.
"Sai dai babban abin lura anan shi ne; tsakanin Kwankwaso da Peter wanene zai haƙura da kwaɗayin son mulkin Najeriya ya bar ma ɗaya takarar shugabancin ƙasar? Lokaci ne kaɗai zai tabbatar da wannan."

Kara karanta wannan

Babu Wannan Maganar: NNPP Ta Karyata Rade-Radin Kwankwaso Ya Zama Mataimakin Obi

Lawan ya tsallake rijiya da baya, sunansa ya maye gurbin na Machina a matsayin dan takarar sanata na APC

A wani labarin, mun ji cewa an bayyana sunan shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa na jam’iyyar the All Progressives Congress (APC) a zaben 2023.

Lamarin na zuwa ne yan awanni bayan Bashir Machina, wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC na kujerar, ya jadadda cewa ba zai janyewa shugaban majalisar dattawan ba.

Lawan dai ya yi takarar tikitin shugaban kasa na jam’iyyar APC sannan awanni kafin fara zaben fidda gwanin sai shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu ya sanar da shi a matsayin dan takarar maslaha na jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel