Gwamna Zulum ya naɗa sabbin kwamishinoni 20, ya tura sunayen su ga Majalisar Borno

Gwamna Zulum ya naɗa sabbin kwamishinoni 20, ya tura sunayen su ga Majalisar Borno

  • Gwamnan Babagana Umaru Zulum ya gabatar wa majalisar dokokin Borno sunayen mutum 20 da zai naɗa kwamishinoni
  • Zulum ya sallami mambobin kwamitin zartarwan jihar ne a watan da ya gabata yayin da APC ta fara gudanar da zaɓen fidda yan takara na zaɓen 2023
  • Sabuwar tawagar mutanen da Zulum ya zaɓo sun kunshi da yawa daga cikin tsofaffin kwamishinonin da ya sallama a baya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya gabatar da sunayen sabbin kwamishinoni 20 da yake son naɗawa ga majalisar dokokin jihar don tantance su, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya rushe mambobi 20 na majalisar zartarwarsa a watan da ya gabata lokacin da jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ke gudanar da tarukan zaɓen fidda yan takararta na zaɓen 2023 da ke tafe.

Kara karanta wannan

Babagana Kingibe ya aika sunayen mutum 3 ga Tinubu ya zabi abokin takara harda tsohuwar minista ciki

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum.
Gwamna Zulum ya naɗa sabbin kwamishinoni 20, ya tura sunayen su ga Majalisar Borno Hoto: Professor Babagana Umaru Zulum MNI/facebook
Asali: Facebook

Yayin da yake gabatar da jerin sunayen sabbin kwamishinonin ga majalisar dokokin Borno jiya Talata, gwamnan ya ce wasu tsaffin kwamishinonin sun samu shiga cikin sabuwar tawagar.

Sunayen mutum 20 da Zulum ya gabatar wa majalisa

Jaridar da tattaro cewa daga cikinn sunayen da Zulum ya gabatarwa majalisa, mutum uku ne sabbi yayin da sauran 17 suna cikin tsofaffin da ya sallama a baya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sabbin da gwamnan ya zaɓa sune Farfesa Mohammed Arabi, Pogu Lawan Chibok da kuma Ali Bunu Mustapha.

Sauran mutum 17 daga cikin 20 da suka rasa aikin su baya, waɗan da suka sake shiga sabuwar tawagar sun haɗa da, Mustapha Gubio, Adamu Lawan, Yerima Saleh, Lawan Wakilbe, da Kaka Shehu Lawan.

Sai kuma Abacha Ngala, Isa Haladu, Sugum Mele, Zuwaira Gambo, Tijjani Goni, Babagana Malumbe, da kuma Yerima Kareto.

Saina Buba, Yuguda Saleh, Buba Walama, Abubakar Tijjani da kuma Babakura Abba Jato duk suna cikin tsofaffin kwamishinonin da Allah ya sake ci da su a sabbin da Zulum ya gabatar wa majalisar dokokin Borno.

Kara karanta wannan

Ekiti 2022: Jerin sunayen yan takara 16 da za su fafata a zaben gwamna

A wani labarin na daban kuma Bayan wani kazamin artabu, Sojoji sun samu gagarumar nasara kan yan ta'adda a Borno

Jami'an tsaro sun yi nasarar halaka yan ta'addan kungiyar ISWAP da dama a yankin Gurzum da ke jihar Borno.

Hukumar sojojin Najeriya, ranar Laraba da safe, ta bayyana cewa dakarun sun lalata kasuwa da sansanin yan ta'addan yayin samamen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel