Babagana Kingibe ya aika sunayen mutum 3 ga Tinubu ya zabi abokin takara harda tsohuwar minista ciki

Babagana Kingibe ya aika sunayen mutum 3 ga Tinubu ya zabi abokin takara harda tsohuwar minista ciki

  • Gabannin cikar wa’adin da INEC ta bayar don jam’iyyun siyasa su gabatar da abokan takarar su, Tinubu da APC suna cikin tsaka mai wuya
  • Ana cikin haka ne, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babagana Kingibe ya gabatar da sunayen wasu mutane uku don a zabi daya cikinsu
  • Mataimakiyar babban sakataren majalisar dinkin duniya, Amina J. Mohammed, na daya daga cikin sunayen da Kingibe ya mikawa Tinubu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babagana Kingibe, ya mika wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, sunayen mutane uku don ya zabi abokin takara a cikinsu.

Kingibe wanda ya kasance abokin takarar marigayi MKO Abiola a zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yuni 1993, ya mika sunayen ga gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, don ya gabatarwa Tinubu domin a tantance.

Kara karanta wannan

Kusoshi a Jam’iyya sun dage Tinubu ya dauki Mataimaki daga mutum 2 a Gwamnatin Buhari

Asiwaju Bola Tinubu tare da uwargidarsa a zaune cikin taron jama'a
Babagana Kingibe ya aika sunayen mutum 3 ga Tinubu ya zabi abokin takara harda tsohuwar minista ciki Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, jerin sunayen na dauke da sunan:

1. Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Mataimakiyar babban sakataren gwamnatin tarayya, Amina J. Mohammed

3. Jami’in hulda da jama’a na majalisar dokokin kasar a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo na farko, Kashim Ibrahim-Imam

Su dukka ukun wadanda suka kasance Musulmai sun fito ne daga yankin arewa maso gabas. Kuma zabin ya zo ne a daidai lokacin da cece-kuce kan yunkurin APC na cike tikitin Musulmi da Musulmi.

A cewar jaridar, wata majiya ta kusa da dan takarar shugaban kasar ta bayyana cewa sun kadu a lokacin da tsohon sakataren gwamnatin ya gabatar da sunayen.

Majiyar ta ce:

“Da gaske ne Ambasada Babagana Kingibe ya mikawa Gwamna Atiku Bagudu sunaye uku don ya mika wa Asiwaju domin ya duba a zabi mataimakin shugaban kasa.”

Kara karanta wannan

Jerin sunayen tsoffin masu takara da Tinubu ya ziyarta tun bayan da ya mallaki tutar APC

Wata majiya ta kuma bayyana cewa har yanzu suna kokarin gano a wani dalili Kingibe yake zabar wani.

Majiyar ta ce:

“Duk da cewa yana cikin na kewaye da gwamnatin, abin da ke a fili shi ne, suna da wani dan takarar shugaban kasa na daban wanda bai yi nasara ba... Don haka mun ji takaicin yadda ya mika sunayen wasu ga Asiwaju ganin cewa ba ya rike da kowani matsayi. Muna zargin cewa ba shi kadai ba ne a wannan yunkuri.”

Ba Mu Yarda Da Musulmi 2 Ba: Kungiya Ta Bayyana Kirista Da Ya Dace Tinubu Ya Dauka a Matsayin Mataimaki a 2023

A wani labarin, kungiyar matasan Kudu da Arewa, 'The Southern-Northern Progressive Youth Congress' ta soki shirin da ake hasashen jam'iyyar APC na yi na zabarwa dan takarta, Asiwaju Bola Tinubu, wani musulmi a matsayin mataimaki a zaben 2023.

Kungiyar cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Nsebabi Brownson da Sakatarenta Bashir Aliyu Galadanci, sun goyi bayan a zabi Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Boss Mustapha a matsayin mataimakin Tinubu, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Kayi watsi da maganar addini ko kabila wajen zaben mataimakinka: Mataimakan gwamnoni ga Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel