Adam Zango ya saki zafafan hotunansa tare da amaryarsa yayin da suka cika shekaru 3 da aure

Adam Zango ya saki zafafan hotunansa tare da amaryarsa yayin da suka cika shekaru 3 da aure

  • Fitaccen dan wasa kuma mawakin Hausa, Adam A. Zango ya yi murnar cikarsu shekaru uku da sahibarsa, Safiya Chalawa
  • Zango ya nuna farin ciki cewa duk da tarin kalubalen da suka fuskanta a rayuwar aurensu, ga shi tafiya ta fara mika
  • Ya kuma saki wasu zafafan hotunansu a shafinsa na soshiyal midiya, inda ya rubuta wasu zantuka masu ratsa zuciya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu ne shahararren dan wasan nan na Hausa kuma mawakin zamani, Adam A. Zango ya cika shekaru da auren amaryarsa, Safiya Chalawa.

Adam Zango ya raya wannan rana ta musamman inda ya saki wasu zafafan hotunansa da matar tasa domin murnar wannan tafiya da ta fara mika a rayuwarsu.

Hotuna: Adam Zango ya yi murnar cika shekaru 3 da auren sahibarsa, Safiya Chalawa
Hotuna: Adam Zango ya yi murnar cika shekaru 3 da auren sahibarsa, Safiya Chalawa Hoto: adam_a_zango
Asali: Instagram

Ana ganin wannan murna tasa ba zai rasa nasaba da yadda suka shafe tsawon shekaru uku ba tare da an ji kansu da amaryar tasa ba sakamakon lakabi da ake masa da mai yawan auri-saki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye daga takara, ya fice daga jam'iyyar APC

Mawakin ya kuma nuna godiya ga Allah a kan yadda suka iya kaiwa war haka duk da tarin kalubale da suka dunga fuskanta tun daga ranar da aure ya kullu a tsakaninsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya rubuta a shafinsa na Instagram:

“Ma shaa Allah, aurenmu ya cika shekaru uku a yau! Ina matukar farin ciki da ganin cewa mun tsallake duk wasu kalubale da suka tunkare mu tun daga ranar da nace: “Eh na yarda”. Sai an daure an kuma yi hakuri sannan ake samun farin ciki a tsakanin ma’aurata. Ina fatan za mu ci gaba da rike soyayyar da hakuri wacce ta haifar da wannan aure mai cike da farin ciki yayin da muke ci gaba da rayuwa a tare. Ina tayamu murnar zagayowar shekara!"

Mabiyansa sun yi martani

iam_oga_abdul ya yi martani:

Kara karanta wannan

Wata mata ta amince ta biya kudi N40,000 don mijinta ya rubuta mata takardar saki

"Masha'allah❤️ Allah yakara sanya albarka"

abbakar8324 ya ce:

"Kaga Allah yakamaka dayabaka yara mata saikadena auri ski sbd idan aka auri yarka aka saketa xakaji yanda iyayen wancen sukaji"

anas_fresh_ ya ce:

"Masha allah❤❤ masu baki da kunu ya ranku"

yerima_shettima ya yi martani:

"Masha Allah kanina"

Manyan jaruman Kannywood 5 da suka yi tashe a farkon 2000

A gefe guda, masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, tana daddiyar tarihi a kasar Hausa, kuma ba za a taba bayar da wannan tarihi ba tare da an ambaci sunayen wasu tsoffin jarumai mata da suka zamo madubin dubawa ga masu tasowa ba.

Duk da cewar babu ingantattun kayan aiki na zamani a wancan lokaci, wadannan jarumai sun jajirce tare da taimakawa matuka wajen daukaka sunan masana’antar har ta kai inda take a yanzu.

A wannan zaure, Legit Hausa ta zakulo maku wasu manyan jarumai mata 5 da tauraronsu ya haska sosai a duniyar fina-finan Hausa cikin shekara ta 2000.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da aka binne Bahaushiyar da IPOB suka kashe da yaranta 4 a Anambra

Asali: Legit.ng

Online view pixel