Allah ya yiwa dan mataimakin gwamnan jihar Yobe rasuwa a hatsarin mota

Allah ya yiwa dan mataimakin gwamnan jihar Yobe rasuwa a hatsarin mota

  • Allah ya yiwa daya daga cikin ‘ya’yan mataimakin gwamnan jihar Yobe, Alhaji Barde Gubana, rasuwa
  • Dan Gubana mai shekaru bakwai a duniya ya rasu ne sakamakon hatsarin mota a hanyar Maiduguri zuwa Kano a ranar Asabar 11 ga watan Yuni
  • Lamarin ya taba mataimakin gwamnan sosai yayin da ya ce zai ci gaba da tuna shi a matsayin na kusa da shi sosai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yobe - Mataimakin gwamnan jihar Yobe, Hon. Idi Barde Gubana, ya rasa dansa a wani hatsarin mota da ya afku a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni.

A cikin wata sanarwa dauke da sakataren labaransa, Hussaini Mai Suleh, a Damaturu, ya ce yaron mai shekaru bakwai wanda ya kasance takwaran Gwamna Mai Mala Buni ya rasu ne a hatsarin mota wanda ya wakana a hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

Allah ya yiwa dan mataimakin gwamnan jihar Yobe rasuwa a hatsarin mota
Allah ya yiwa dan mataimakin gwamnan jihar Yobe rasuwa a hatsarin mota Hoto: @BuniMedia, Hussaini Mai Suleh
Asali: Facebook

Ya ce tuni aka binne yaron daidai da koyarwar addinin Musulunci a fadar Mai na Fune a garin Damagum da ke karamar hukumar Fune, jaridar Leadership ta rahoto.

Da yake martani kan lamarin, mataimakin gwamnan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Zan ci gaba da tunanwa da shi a matsayin makusancina."

Manyan jami'an gwamnati da sauran masu fada aji sun ziyarci gidan mataimakin gwamnan domin taya iyalan alhinin rashin da suka yi.

Sanarwa ta ce:

“Allah ya yiwa dan mai girma mataimakin gwamna Alhaji Idi Barde Gubana (Wazirin Fune) rasuwa. Marigayin ya kasance takwaran mai girma Gwamna Mai Mala Buni (Chiroman Gujba.
Ya rasu a safiyar ranar Asabar a wani hatsarin mota a hanyar Maduguri-Kano.
“Shekarar yaron 7 kuma tuni aka binne shi daidai da koyarwar addinin Musulunci a fadar Mai Fune a garin Damagum, karamar hukumar Fune,

Kara karanta wannan

Neman Mataimkin Atiku: PDP Ta Kafa Kwamiti A Yayin Da Wike Da Okowa Ke Neman Zama Mataimakin Shugaban Kasa

“Allah ya tanadi gida a Al-janna ga wadanda suka rasa yaransu suna kanana kuma suka yi hakuri.
“Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, idan dan mutum yam utu, Allah zai cewa mala’ikunsa, kun dauki ran dan bawana.
“Sai su ce Eh
“Sai Yace kun dauke sanyin idanuwansa?
“Sai suce eh.
“Sai yace mai bawana ya ce?
“Sai sucde ya kasaita ka sannan ya ce "INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRAJIUN"
“Sai Allah ya ce, ku ginawa bawana gida a Aljanna sannan ku kira shi gidan yabo. (Al- Thirmidhi 942)
"Allhau Akbar
“Allah ya sanyawa mai girma gwamna da iyalansa juriya.”

Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare

A wani labarin, mun ji cewa an sace matasa akalla guda 50 a hanyar Sokoto-Gusau a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Burin 2023: Ajandoji 7 da Bola Tinubu ke da burin yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Kamar yadda Legit.ng ta tattaro, yawancin mutanen da aka sace yan kasuwa ne da ke sana’ar siyar da wayoyi a shahararriyar kasuwar nan da Gusau da ake kira Bebeji Plaza.

An kuma tattaro cewa lamarin ya afku ne da yamma yayin da mutanen da aka sace ke a hanyarsu ta komawa Sokoto inda suka halarci daurin auren daya daga cikin abokan sana’arsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel