Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare

Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare

  • Wani abun bakin ciki ya sake samun Najeriya bayan an yi garkuwa da wasu yan kasuwa 50 a Gusau, jihar Zamfara
  • An tattaro cewa mutanen da abun ya ritsa da su san kasance yan kasuwa da ke sayar da wayoyi a wata shahararriyar kasuwar wayoyi ta Bebeji Plaza
  • Sai dai kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce mutum 20 daga cikin 50 da aka sace sun kubuta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Wani rahoto da ke zuwa mana ya tabbatar da sace matasa akalla guda 50 a hanyar Sokoto-Gusau a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni.

Kamar yadda Legit.ng ta tattaro, yawancin mutanen da aka sace yan kasuwa ne da ke sana’ar siyar da wayoyi a shahararriyar kasuwar nan da Gusau da ake kira Bebeji Plaza.

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

Yan bindiga sun yi garkuwa da matasa 50 a hanyar Sokoto-Gusau
Yan bindiga sun yi garkuwa da matasa 50 a hanyar Sokoto-Gusau Hoto: Ahmad Khaleel
Asali: Facebook

An kuma tattaro cewa lamarin ya afku ne da yamma yayin da mutanen da aka sace ke a hanyarsu ta komawa Sokoto inda suka halarci daurin auren daya daga cikin abokan sana’arsu.

Wani ganau ya ba da labarin lamarin

Da yake tabbatar da lamarin ga wakilin Legit.ng, daraktan hulda da jama’a na kungiyar yan kasuwar Bebeji Plaza, Zulkifilu Muhammad wadanda lamarin ya ritsa da su suna tafiya a motocin basu uku lokacin da masu garkuwa da mutanen suka kama su a kusa da garin Tureta hanyar Sokoto/Zamfara, iyakar jihohin biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mai suna Usman ya fada ma Legit.ng cewa ya shiga dimuwa kan lamarin yayin da yake kuma rokon gwamnatin jihar Zamfara da hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa don ceto wadanda aka sace cikin gaggawa.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da lamarin, ta ce mutum 20 sun samu yanci

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Bayan kwanaki 74, an sako mutum 11 cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna

A halin da ake ciki, rundunar yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an saki mutum 20 cikin mutanen da aka sace.

Kakakin yan sandan rundunar, SP Shehu Muhammad ya sanar da wakilin Legit.ng a Zamfara cewa cikin mutum fiye da 50 da aka sace 20 sun samu yanci bayan maharan sun yi watsi da su a hanya.

Ya ce rundunar ta tura tawagar bincike da ceto zuwa yankin domin su ceto sauran mutanen.

An jikkata wasu da dama yayin da rikici ya barke tsakanin Hausawa da Inyamurai yan kasuwa a Edo

A wani labari na daban, mun ji cewa an samu barkewar rikici a safiyar ranar Asabar, 11 ga watan Yuni a garin Benin, jihar Edo, yayin da fusatattun matasa wadanda yawancinsu yan kasuwa ne a sabuwar kasuwar Benin suka tashi hankali bayan wani dan kasuwa daga arewa ya farma takwaransa na Igbo da adda.

Kara karanta wannan

An jikkata wasu da dama yayin da rikici ya barke tsakanin Hausawa da Inyamurai yan kasuwa a Edo

Rigima ya fara ne bayan wani dan sabani da ya shiga tsakanin yan kasuwar biyu. An ce dan Igbon ya umurci Bahaushen da ya bar masa gaban shagonsa, jaridar Punch ta rahoto.

An tattaro cewa ana haka ne sai Bahaushen dan kasuwan wanda hakan bai yi masa dadi ba ya zaro addansa sannan ya caki Inyamurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel