Alarammoni da wasu dubbannin mutane sun gudanar da Addu'a kan zaɓen 2023 a Kano

Alarammoni da wasu dubbannin mutane sun gudanar da Addu'a kan zaɓen 2023 a Kano

  • Dubbanin musulmai a Kano sun gudanar da Addu'o'in samun zaman lafiya da gudanar da zaɓen 2023 cikin kwanciyar hankali
  • Mutanen da suka haɗa da Alarammoni sun kuma yi Addu'o'in Allah ya zaɓa wa Najeriya shugaban ƙasa nagari
  • Ƙungiyar mahaddata Alƙur'ani KURAN da kungiyar matasa da mata YOWPA da ta yan kasuwa AMATA ne suka shirya taron

Kano - Aƙalla Musulmai 3,000 a jihar Kano suka gudanar da taron Addu'a na musamman domin samun zaman lafiya yayin zaɓen 2023 da ke tafe, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Taron Addu'an ya gudana ne a Masallacin Gwano Ɗanzarga da ke Koki Quaters a Kano karƙashin ƙungiyar mahaddata Alkur'ani ta Najeriya (KURAN), kungiyar wayar da kai ta matasa da mata (YOWPA) da gamayyar kungiyar yan kasuwa ta ƙasa (AMATA).

Kara karanta wannan

Tsohon dogarin Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa

Taron Addu'a.
Alarammoni da wasu dubbannin mutane sun gudanar da Addu'a kan zaɓen 2023 a Kano Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Da yake jawabi a wurin taron, shugaban ƙungiyar KURAN, Gwani Lawi Gwani Danzarga, ya shaida wa manema labarai cewa sun gudanar da Addu'a ne domin samun zaman lafiya a Najeriya.

Ya ce sun yi Addu'ar fatan yin sahihi kuma amintaccen zaɓe cikin kwanciyar hankali duba da ƙaruwar tsoro, ɗar-ɗara da kuma tashin hankali a abubuwan da ke zuwa gabanin zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Kowa na da masaniyar halin rashin tsaron da ƙasar nan ke ciki kuma ga zaɓen 2023 na tunkaro wa, saboda haka akwai buƙatar yin addu'a don samun zaman lafiya mai ɗorewa."
"A Musulunci mun yi imanin cewa ba abun da ya gagari Allah SWT. Saboda haka abun da muka yi zaburar wa ce ga yan uwa musulmai su miƙa lamarin su ga Allah ya zaɓa mana shugaba, wanda zai ɗauki alhakin jagorancin ƙasar mu."

Kara karanta wannan

Daga karshe, Shugaba Buhari ya magantu kan nasarar Bola Tinubu a zaɓen fidda gwanin APC

"Allah ya san halin da muke ciki, mun miƙa lamarin gare shi ya zaɓa mana shugaba nagari da zai jagorance mu zuwa hanya madaidaiciya kuma ya ɗaga Najeriya zuwa babban matsayi ba tare da duba yankin da ya fito ba."

Ya kamata matasa su hankalta - YOWPA

A jawabinta shugabar ƙungiyar YOWPA, Hajiya Asmau Sarki Mukhtar, tace sun haɗa kai da wasu ƙungiyoyi domin wayar da kan matasa da mata su fito a dama da su a siyasa.

"Mun kirkiro shirin wayar da kan matasa kar su bari a yi amfani da su wajen ta da rikici da hana zaɓe."

Ta roki iyayen gida yan siyasa da su ji tsoron Allah, su mai da hankali wajen tabbatar da zaman lafiya kafin da kuma bayan zaɓe.

A wani labarin na daban kuma Bayan shan kaye hannun Tinubu, Tsohon ministan Buhari ya lashe tikitin sanata a APC

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar SDP ta sanar da sakamakon zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa

Tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya lashe tikitin takarar sanata na jam'iyyar APC.

Akpabio, wanda ya janye wa Tinubu takara a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa, ya samu nasara ne a zaben da aka canza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel