Bola Tinubu ne ɗan takarar da yafi cancanta ya gaji kujerata a 2023, Buhari

Bola Tinubu ne ɗan takarar da yafi cancanta ya gaji kujerata a 2023, Buhari

  • Shugaba Buhari ya yi magana kan nasarar Tinubu, ya ce shi ne ɗan takarar da ya dace ya karɓi Najeriya a 2023
  • Sai dai shugaban kasan ya gargaɗi jam'iyyar APC cewa dole kowa ya maida wuƙarsa kube, a haɗa kai don tunkarar zaɓe don cin nasara
  • Ya ce lokaci ya yi da APC zata cigaba da rike matsayinta na jam'iyyar da babu kamarta wajen cika muhimman bukatun yan ƙasa

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a matsayin ɗan takarar da ya dace da Najeriya a 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tinubu, ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ranar Laraba bayan kammala zaɓen fidda gwani a Eagle Square.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar SDP ta sanar da sakamakon zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa

Shugaba Buhari, a wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar, ya taya ɗan takarar APC a zaɓen 2023 murna, inda ya tabbatar masa da samun, "cikakken goyon baya."

Shugaban ƙasa Buhari da Tinubu.
Bola Tinubu ne ɗan takarar da yafi cancanta ya gaji kujerata a 2023, Buhari Hoto: @Buhari Sallau1
Asali: Facebook

Buhari ya nuna yaƙinin cewa Tinubu zai kare tare da haɓaka cigaban demokaraɗiyya da muhimman ayyukan raya ƙasa da ya fara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban ƙasa ya ƙara da cewa a yanzun APC zata dawo gida ta haɗa kanta, sannan ta marawa ɗan takarata baya domin cimma nasara a babban zaɓen 2023.

Buhari ya ce:

"Bayan ayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara yana da cikakken goyon bayan mu mara adadi. Yanzun wajibi APC ta haɗa kai ta marawa ɗan takarar mu baya don cimma nasara a zaɓen 2023 saboda gwamnatin mu ta cigaba da tsare yankuna, haɓaka tattalin arziki da yaƙar cin hanci."

Kara karanta wannan

Magajin Buhari: Zamu shiga tasku idan muka gaza zakulo ɗan takara mai ƙarfin Atiku, Gwamnan APC

"Lokacin zaɓe an samu rabuwar kai da saɓani tsakanin yan takara kuma yanzun ya wuce, wajibi mu haɗa kan mu domin ta haka ne kaɗai APC zata cigaba da zama jam'iyyar da bata da tsara wajen cika muhimman burikan yan Najeriya."
"Lokaci ya yi da zamu mance komai domin mun yarda cewa babu kamar APC wajen warware muhimman matsalolin yan Najeriya, amma domin tabbatar da haka sai mun haɗa kai."

Da Tinubu muka kafa tafiyar tun 2013 - Buhari

Shugaban ƙasan ya ƙara da cewar tafiyar da suka fara tun shekarar 2013 ta fi karfin dai-daikun mutane, kuma tare suka kafa tarihi na lallasa jam'iyyar da ke kan mulki.

"Tare muka kafa tarihi na zama jam'iyyar ta farko a tarihi da ta kwace mulki daga hannun jam'iyya me mulki kuma ɗan takararta ya karbi mulki ta hanyar da Demokaraɗiyya ta tanada."
"Muna da yaƙini mai karfi cewa Tinubu zai kare tare da haɓaka cigaba da ayyukan raya kasar da muka gudanar. Shi ne ɗan takarar da ya dace da cika bukatun yan Najeriya."

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC bai hakura ba, zai gabatar da sunan wanda yake so ga Buhari don goya masa baya

A wani labarin kuma Shugaba ƙasa Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi na musamman ranar Lahadi

Shugaba Muhammadu Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi ta musamman misalin karfe 7 na safiyar Lahadi, 12 ga watan Yuni, 2022.

Ministan Labarai, Lai Mohammed, ya bayyana hakan yayin hira da yan gidan rediyo ranar Alhamis a Abuja. Yace zai yi jawabin bisa murnar ranar demokradiyya ta shekarar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel