Jam'iyyar SDP ta sanar da ɗan takarar da ya lashe tikitin shugaban kasa

Jam'iyyar SDP ta sanar da ɗan takarar da ya lashe tikitin shugaban kasa

  • Jam'iyyar SDP ta bi sahun sauran jam'iyyu yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen 2023 da ke tafe
  • A ranar Laraba, SDP ta sanar da Adewole Adebayo, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa bayan ya lashe zaɓen fidda gwani
  • Prince Adebayo, Ɗan kasuwa a jihar Legas, ya ce lokaci ya yi da yan Najeriya zasu gane me ke musu ciwo, su canza gurɓatattun shugabanni

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ɗan kasuwa a jihar Legas, Prince Adewole Adebayo, ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na Social Democratic Party wato SDP yayin da ake tunkarar zaɓen 2023.

Adebayo ya samu kuri'u 1,526 a babban taron SDP na ƙasa da ya gudana a Abuja domin zaɓen ɗan takarar da zai rike tutar jam'iyya a zaɓe mai zuwa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Atiku Abubakar ya aike da sakon murna ga Bola Tinubu bayan lashe tikitin APC

Prince Adewole Adebayo.
Jam'iyyar SDP ta sanar da ɗan takarar da ya lashe tikitin shugaban kasa Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Ɗan takarar ya lallasa abokiyar takararsa matashiyar mace, Khadija Lamidi, wacce yayin zaben ta samu kuri'u 83.

Shugaban kwamitin shirya zaɓen, Umar Arɗo, ya bayyana cewa an ƙaɗa kuri'u 1,653, sahihai 1,609 yayin da guda 44 suka lalace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake jawabin godiya, Adebayo ɗan kimanin shekara 54, Lauya kuma me gidan Talabijin ɗin KAFTAN, ya ce nasarar da ya samu wata alama ce da ke nuna cewa mulki zai koma hannun yan Najeriya.

Ya ce lokaci ya yi da yan Najeriyan da ba su samun abun sawa a baka, matasan da suka gama karatu ba aiki ko waɗan da yajin aiki ya rike su, zasu yi amfani da damar demokaraɗiyya.

APC da PDP zasu gane kuren su a 2023 - Adebayo

Ɗan kasuwan ya sha alwashin cewa zai yaƙi mamayar manyan jam'iyyun ƙasar nan APC da PDP a babban zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

NNPP 2023: Da zaran na zama gwamnan Kano masu cin hanci sun shiga uku, Abba Gida-Gida

Vanguard ta ruwaito Adebayo na cewa

"Zamu tallata hajar mu gida-gida, runfunan zaɓe, kowace gunduma, kowace ƙaramar hukuma, kowace jiha, kowace shiyya da sassan ƙasar nan baki ɗaya."
"Zamu fito mu nuna wa yan Najeriya cewa abinci, ruwa, wuta, wurin zama, neman lafiya da suke fafutuka a kai, bai dace ace sai sun roƙa ba."

A wani labarin kuma Gwamna ya dakatar ASUU a jiharsa, ya umarci Malaman jami'o'i su koma aiki ko ya ɗau mataki

Gwamnatin jihar Edo ta dakatar da ayyukan dukkan wasu ƙungiyoyi da suka shafi manyan makarantun gaba da Sakandire mallakin jiha.

Gwamnatin karkashin gwamna Godwin Obaseki ta ce duk wani ma'aikaci da yaƙi bin umarni zata sallame shi daga aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel