Taron APC: Deliget din Rivers sun yi hatsari, mutum daya ya mutu

Taron APC: Deliget din Rivers sun yi hatsari, mutum daya ya mutu

  • Deliget din jam’iyyar APC sun yi hatsari a hanyarsu ta komawa jihar Rivers daga Abuja bayan sun halarci zaben fidda dan takarar shugaban kasa
  • An tattaro cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu biyar suka jikkata kuma suna kwance a asibitin koyarwa ta jami’ar Abuja
  • Wani da ya tsallake rijiya da baya a hatsarin, Innocent Amadi, ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace birki ne ya kwacewa direban motar bayan ya kwaso gudu

Abuja - Mutum daya ya mutu bayan wata mota kirar Toyota Sienna da ta kwashi mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga Abuja zuwa jihar Rivers ta yi hatsari.

Daya daga cikin wadanda ke a motar, Innocent Amadi, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a gidan rediyon Port Harcourt, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Saboda budurwa: Fitaccen dan kwallon Arsenal ya tabbatar da karbar addinin Muslunci

Amadi ya ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 8:00 na safiyar Alhamis, 9 ga watan Yuni, a kusa da gidajen ma’aikata na jami’ar Abuja.

Taron APC: Deliget din Rivers sun yi hatsari, mutum daya ya mutu
Taron APC: Deliget din Rivers sun yi hatsari, mutum daya ya mutu Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Mutumin da ya tsira a motar ya ce direban na gudu ne lokacin da ya gaggauta cin birki yayin da wata mota ke gabansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ci gaba da bayyana cewa biyar daga cikin mutane bakwai da ke motar sun jikkata kuma suna samun kulawar likitoci a asibitin koyarwa na jami’ar Abuja.

Ya ce:

“Motarmu ta kwaso gudu. Don haka, akwai wata mota a gabanmu. Saboda direban ya kwaso gudu sai ya kasa daidaita abun, ya ci birki sai kafar motar ta cire.
“Motar ta kife ne. ni ne a gaba. Na fito ba tare da rauni ba. Na daura belit din kujerata. Koda dai mun rasa mutum daya. Mutane biyar sun jikkata.”

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

Zuwa yanzu ba a bayyana wanda ya mutum ba, amma an tattaro cewa sun halarci babban taron fidda dan takarar shugaban kasa da aka kammala ne a Abuja.

Zaben fidda gwanin APC: Deliget din Jigawa ya yanki jiki, ya fadi matacce

A wani lamari makamancin wannan, mun ji cewa daya daga cikin wakilan jam'iyyar APC na Jigawa Alhaji Isah Baba Buji ya rasu yayin da yake wurin taron zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar a Abuja.

Ya fadi ya mutu ne sakamakon bugun zuciya a safiyar ranar Talata a ofishin hulda da jama’a na jihar Jigawa da ke Abuja.

Marigayin dai shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai kula da shiyyar Jigawa ta tsakiya, inji rahoton jaridar The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel