Abubuwa sun tabarbare, Mai dakin Gwamna El-Rufai ta soki sha’anin ilmi a yau

Abubuwa sun tabarbare, Mai dakin Gwamna El-Rufai ta soki sha’anin ilmi a yau

  • Hajiya Ummi El-Rufai ta yi bayani bayan an gyara wata makarantar gwamnati da ke Marabar Jos
  • Ummi El-Rufai ta yaba da yadda aka gyara makarantar firamaren Modern Primary School a Kaduna
  • Uwargidar ta ce idan akwai makarantar gwamnati irin haka, ba za a damu da makarantun kudi ba

Kaduna - Mai dakin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Ummi El-Rufai, ta koka a kan yadda harkar ilmi ta lalace a Najeriya, ta ce abin ya tabarbare sosai.

A ranar Litinin, 6 ga watan Yuni 2022, Daily Trust ta rahoto Hajiya Ummi El-Rufai ta na mai cewa akwai matukar gyara a kan sha’anin ilmi yau a Najeriya.

A cewar Matar Mai girma Nasir El-Rufai, yaran makaranta ba su da damar koyon karatu da kyau.

Ummi El-Rufai ta yi wannan jawabi ne a makarantar firamaren nan ta Fifth Chukker Modern Primary School da aka gina a Marabar Jos da aka gyara.

Rahoton ya ce Fifth Chukker da bankin Access Bank su ka gyara wannan makarantar gwamnati da za ta dauki nauyin ilmin yara 12, 000 ke cikin karkara.

Matar Gwamnan wanda ita ce Jakadar kungiyar UNICEF ta ce makarantar da aka gyara za ta taimaka wajen inganta ilmin yaran da ke rayuwa a kauyuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai dakin Gwamna El-Rufai
Mai dakin Gwamna El-Rufai da Hajiya Ummi El-Rufai Hoto: @ummielrufai
Asali: Facebook

Abubuwa sun canza

A cewar mai dakin Gwamnan na jihar Kaduna, a shekarun baya sun samu ilmi mai nagarta a kyauta, akasin abin ake gani a makarantun zamanin yau.

Ummi El-Rufai ta ke cewa kowa zai yi fatan bada gudumuwarsa a wannan aiki da zai taba rayuwar yara 12, 000 lokacin da harkar ilmi ya shiga ni–‘ya su.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, mai dakin gwamnan ta ce a yau yara ba su da isasshiyar damar daukar darasi, don haka ta ji dadin bude makarantar.

Har ila yau, El-Rufai ta ce idan ana samun irin wadannan makarantun zamani a al’umma, iyaye ba za su damu da tura yaransu zuwa makarantun kudi ba.

500 ta zama 12000

Adamu Attah wanda shi ne ya kafa Fifth Chukker, ya bada labarin yadda aka kawo maganar gyara wannan makarantar gwamnati da ke garin Marabar Jos.

Da farko makarantar ta na daukar yara 500 ne kacal, amma yanzu yara 12000 za su iya karatu. A cikin wadanda suka bada gudumuwar har da kungiyar UNICEF.

Garkuwa da mutane

Abdulkarim Abdulsalam Zaura wanda fitaccen Attajiri kuma ‘dan siyasa ne a jihar Kano ya tashi a ranar Litinin da labarin garkuwa da tsohuwarsa a garin Ungogo.

Dazu mu ka ji cewa an ceto wannan Baiwar Allah bayan kwanaki biyu da jin cewa ‘yan bindiga sun shiga kauyen Rangaza a Kano cikin duhun dare, sun dauke ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel